A Karshe, Kotun Daukaka Kara Ta Yanke Hukunci kan Sahihancin Zaben Ciyamomin Kano
- Kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta soke hukuncin babbar kotun tarayya ta Kano da ya rusa KASIEC da zaɓen ƙananan hukumomi
- Alkalai uku karkashin jagorancin Mai Shari’a Georgewill sun ce kotun jihar Kano ce kaɗai ke da hurumin sauraron irin waɗannan shari’o’i
- Kotun ta tabbatar da sahihancin shugabannin ƙananan hukumomi 44 da suka lashe zaɓen da hukumar KASIEC ta gudanar a 2024
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta soke hukuncin da wata babban kotun tarayya da ke Kano ta yanke, wanda ya soke tsarin hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kano (KASIEC).
Kotun ta kuma soke hukuncin da ya soke zaɓen ƙananan hukumomi da KASIEC ta gudanar a ranar 26 ga Oktoba, 2024 a fadin jihar Kano.

Asali: Twitter
Kotun daukaka kara ta yi hukuncin kan zaben Kano
Hukunci ya fito ne a cikin hukunce-hukunce uku da kotun ta yanke, karkashin jagorancin Mai Shari’a Biobele Georgewill, tare da wasu alkalai biyu, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotun ta bayyana cewa babbar kotun tarayya ba ta da hurumin sauraron ƙorafe-ƙorafe da suka shafi tsarin hukumar zaɓen jihar da cancantar mambobinta.
A bisa haka, kotun ɗaukaka ƙara ta amince da daukaka ƙarar da babban lauyan Kano, majalisar dokokin jihar Kano da kuma hukumar KASIEC suka shigar.
Kotun ta soke karar da aka shigar a gaban babbar kotun tarayya, inda ta ce ba ta da hurumi a kan batun, don haka ta kori shari’ar baki ɗaya.
Kotu ta tabbatar da sahihancin ciyamomin Kano
Kotun ta ce babbar kotun jihar Kano ce kadai ke da hurumin sauraron irin wannan ƙara, don haka ta tabbatar da inganci da sahihancin zaben shugabannin ƙananan hukumomi 44 na Kano.
A wani hukunci na huɗu da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke ranar Juma’a, ta soke wani hukuncin da babbar kotun tarayya ta Kano ta yanke, wanda ya ƙi amincewa da jerin sunayen ‘yan takara da bangaren Rabiu Musa Kwankwaso na jam’iyyar NNPP ya mika wa KASIEC don zaɓen ƙananan hukumomi na baya.

Asali: Facebook
Kotun ta bayyana cewa rikicin shugabancin da ya shafi wace ƙungiya ce ta NNPP ke da sahihin ‘yan takara, ba batun da kotun ke da hurumi a kai ba ne.
Channels TV ta rahoto cewa kotun ta kuma ƙara da cewa batutuwan da suka shafi shugabancin jam’iyya da gabatar da ‘yan takara ba za su iya zama batun shari’a ba.
'Ku amince da shan kaye' Abba ga 'yan adawa
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana ra'ayinsa game da zaɓen shugabannin ƙananan hukumomi da kansiloli da hukumar zaɓe ta jihar ta gudanar.
Yusuf ya ce hukumar KANSIEC ta gudanar da zaɓe cikin sahihanci da lumana, yana mai nuna tabbacin cewa waɗanda aka zaɓa za su wakilci jama’a yadda ya kamata.
Da yake magana bayan kada kuri’arsa a Gwamme, ya ce gwamnati ta ɗauki duk matakan da suka dace don tabbatar da zaman lafiya a fadin jihar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng