Idan har ina raye ba zan taba bari a ci zarafin Buhari a majalisa ba - Inji Yaya Tongo
Daya daga cikin 'yan majalisar tarayya masu biyayya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, Honarabul Yaya Bauchi Tongo ya bayyana cewa shi da takwarorin sa na majalisa masu kare martabar Buhari ba za su taba bari a ci zarafinsa ko ci masa fuska a majalisa ba.
Yaya Tongo, wanda ke wakiltar kananan hukumomin Gombe, Funakaye da Kwami dake jihar Gombe, ya kara da cewa ba komai ya sa suke biyayya ga shugaba Buhari ba a majalisa illa kyawawan manufofi da kudirorin da yake da su ga Najeriya da al'ummarta.
"Ko don ingataccen tsaro da aka samu a kasar nan, musamman a yankin Arewa maso gabas da ake fama da rikicin Boko Haram, ya zama wajibi mu marawa Buhari baya.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Osinbajo ya jagoranci zaman majalisar zartarwa
"A baya ba ma iya shiga cikin cinkoson jama'a a Arewacin kasar nan, saboda fargabar tashin bam, amma cikin ikon Allah Buhari ya zama silar kawo karshen wannan fargaba", inji Tongo.
A halin da ake ciki, shugaban kasa Buhari na birnin Landan inda yake hutu, kafin tafiyarsa ya mika ragamar mulki ga mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng