Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci
- A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala
- Musulmai sun dauki wannan rana da muhimmancin gaske
- Ranar Juma'a na daya daga cikin Ranakun Idin Musulunci
A yau kuma mun koma zauren Addinin Musulunci ne inda mu ka tabo kadan daga cikin falalar wannan rana ta Juma'a. Akwai sunnoni da dama da ake so a aikata a wannan rana.
1. Karbar addua
Ya zo a hadisin Bukhari da Muslim cewa akwai wani lokaci a wannan Rana da ba a maida addua da zarar mutum yayi ta. Wannan na daga cikin falalar wannan Rana.
KU KARANTA: Wata Musulma ta taka rawar gani a gasa
k8k8. Ladar zam8kk
Duk wanda ya isa masallaci kafin Liman ya iso ya gabatar da huduba yana da matukar lada wanda Mala'iku ne za su sa shi cikin wani littafi. Iya saurin mutum iya ladar da zai samu Inji Manzon Allah SAW.
3. Kariya daga Dujjal
Duk wanda ya karanta Suratul Kahf zai samu tsari daga fitinannen da zai zo a karshen zamani watau Dujjal. Haka kuma zai samu falala mai yawa har zuwa Juma’ar wata makon.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Legit.ng ta kai wa wata Bawar Allah ziyara
Asali: Legit.ng