'Yan Sanda Sun Gano Maboyar Makamai a Jihar Arewa, Sun Cafke Wadanda Ake Zargi

'Yan Sanda Sun Gano Maboyar Makamai a Jihar Arewa, Sun Cafke Wadanda Ake Zargi

  • An gano wasu tarin alburusai na bindigar AK47 da aka ɓoye wani gidan gonar kiwon kaji da ke a jihar Neja
  • Rundunar ƴan sandan jihar ita ce ta jagoranci samamen gano alburusan har guda 350 a gidan gonar wanda yake a ƙaramar hukumar Tafa ta jihar
  • A yayin samamen da aka kai a gidan gonar, an cafke wasu mutun huɗu da ake zargi ciki har da manajan gidan gonar da wasu ma'aikata guda biyu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Neja - Rundunar ƴan sandan jihar Neja ta gano wasu harsasai na bindigar AK-47 guda 350 a wani gidan gonar kiwon kaji a jihar.

Rundunar ƴan sandan ta kuma cafke wasu mutum huɗu a gidan gonar wanda yake a kan titin Sabon-Wuse-Garam a ƙaramar hukumar Tafa ta jihar Neja.

Kara karanta wannan

An maka gwamnonin Najeriya da Wike kara a gaban kotu kan abu 1

'Yan sanda sun gano alburusai a Neja
'Yan sanda sun gano alburusan AK47 a Neja Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Hanyar dai ita ce ta zuwa garin Bwari dake cikin babban birnin tarayya Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani ɗan banga ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa an kama mutum huɗu, da suka haɗa da manajan gonar, wasu ma’aikata biyu da kuma wani baƙo a yayin samamen.

Ya ce babu tabbas ko alburusan na da alaƙa da ayyukan ƴan bindigan da ke yankin ko kuma an shirya yin safarar su zuwa wani waje ne daban.

Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?

Legit Hausa ta tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar Neja, Wasiu Abiodun, domin samun ƙarin bayani kan lamarin.

Sai dai kakakin rundunar ƴan sandan bai dawo da amsar saƙon da aka tura masa ta wayarsa ba har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.

Ƴan Sanda Sun Cafke Dattawa 2 a Bayelsa

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun halaka shugaban al'umma a wani sabon hari

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar ƴan sandan jihar Bayelsa ta cafke wasu dattawa mutum biyu kan yunƙurin sace ƙanin Gwamna Duoye Diri na jihar Bayelsa.

Mutanen biyu masu suna Lucky Oghenebrume mai shekaru 53 da Omobowho Okpowodo mai shekaru 52, sun shiga hannu ne bayan an gano sun shirya maƙarƙashiyar sace Ayama wanda aka fi sani da Americana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel