Kungiyar ESN Ta Kashe Bokanta Bisa Yin Tsafin da Bai Yi Tasiri Kan ’Yan Sanda Ba

Kungiyar ESN Ta Kashe Bokanta Bisa Yin Tsafin da Bai Yi Tasiri Kan ’Yan Sanda Ba

  • Rahoto ya bayyana cewa, mambobin kungiyar ta'addanci ta ESN ta kashe bokanta saboda wasu dalilai
  • Rahoton 'yan sanda ya ce, sun kashe boka ne saboda layar da ya yi musu ba ta yi tasiri ba kwata-kwata
  • Sun kone shi kurmus, hakazalika sun bankawa gidansa wuta bayan yi masa kisan gilla

Mambobin haramtacciyar kungiyar tsaro ta Gabas (ESN) sun harbe wani mutum, mai suna Paschal Okeke, wanda ke kera “layar cin nasara” ga kungiyar saboda gazawar layarsa wajen karesu na tsawon shekaru, in ji ‘yan sanda a jihar Imo.

Wata sanarwa daga ‘yan sanda ta ce, kungiyar ta fusata da cewa layar, wanda ya kamata ta sa ba za a iya cin nasara a kansu ba kuma su tsere wa farmakin jami’an tsaro ba ta yi wani tasiri ba.

‘Yan sanda sun ce kisan ya biyo bayan samun nasarar 'yan sanda na kai samame a maboyar kungiyar da kuma ragargazar mambobin haramtacciyar kungiyar IPOB, Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA: Shinkafa Ta Wadata a Najeriya, Saura a Fara Fitarwa Kasashen Waje, in Ji RIFAN

'Yan ta'addan ESN sun kashe Bokansu saboda tsafinshi na bacewa yaki musu aiki
Mambobin haramtacciyar kungiyar tsaro ta ESN a yankin kudu maso gabas | Hoto: sunnewsonline.com
Asali: UGC

'Yan sanda sun ce kisan ya faru ne a ranar 25 ga Yuni, kuma bayan harbe shi, sun kone gawarsa kurmus, hakazalika sun cinna wa gidansa wuta.

An fara amfani da tsafi a kudu maso gabas don magance matsalar tsaro

Wani rahoton da Daily Trust ta wallafa ya nuna cewa an ajiye wani kambun tsafi a gaban babban ofishin 'yan sanda na jihar Abia da nufin kare hare-haren 'yan bindiga.

An gano cewa mazauna Bende road a Umuahia, babban birnin jihar, a ranar Talata 22 ga watan Yuni sun farka sun ga an ajiye kambun tsafin a inda aka takaita zirga-zirgan mutane da ababen hawa.

Duk da cewa a yanzu Legit.ng bata samu damar tabbatar da lamarin ba, rahoton da jaridar ta wallafa ya ambaci cewa mazauna unguwar sunyi ikirarin cewa an ajiye kambun tsafin ne don kare jami'an tsaro daga 'yan bindiga.

KU KARANTA: Muna Godiya: Ganduje Ya Jinjina Wa Sojoji Bisa Kare Dajin Falgore da Jihar Kano

A wani rahoton, Gwamnatin jihar Oyo da ke kudancin Najeriya ta bai wa bokayen da ke jihar umarnin su dauki kowane irin mataki domin kawo karshen matsalar tsaro a jihar.

Legit.ng Hausa ta ruwaito ta BBC na cewa, kwamishinan Yada Labarai na jihar, Dr Wasiu Olatunbosun ne ya bayar da umarnin ga kungiyar masu maganin gargajiya ta jihar a madadin Gwamna Seyi Makinde na Oyo.

Ya tabbatar musu da cewa gwamnatin jihar za ta ba su dukkan goyon bayan da suke bukata domin taimakawa wajen samar da maganin matsalar tsaro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel