Auren Gata: Abin da Hisbah za Ta Yi wa Maza da Mata 3,000 a Kano kafin a Biya Sadaki
- Hukumar Hisbah ta Kano ta ɗauki harama game da daura auren gata ga mutane 3,000 da za su ci gajiyar shirin daga ranar Litinin 8 ga watan Yuni, 2026
- Za a gudanar da shirin ne a ƙananan hukumomi 24 da ke faɗin jihar Kano inda ma'auratan suka fito domin tabbatar da an yi komai lafiya
- Hukumar Hisabah ta yi gargaɗin cewa duk wanda ya kauracewa wannan mataki da aka fito da shi, ya rasa damar shiga tsarin auren gatan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kammala shirye-shiryen gudanar da gwajin lafiya a kan ma’aurata 3,000 da ake sa ran za su amfana da shirin auren gata da gwamnatin jihar ta shirya.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Katsina ta yi magana kan sace Janar da matarsa, ta fadi kokarin da take yi
Mataimakin Babban Kwamandan Hisbah, Sheikh Mujahedeen Aminudeen, ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da manema labarai ranar Lahadi 7 ga watan Yuni, 2026.

Source: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa Sheikh Mujahedeen Aminudeen ya ce za a fara gudanar da gwajin lafiyar ne daga ranar Litinin, 8 ga watan Yunin 2026, a ƙananan hukumomi 24 na jihar.
Kano: Za a gwada masu shirin auren gata
A rahoton jaridar Punch, jagora a hukumar ta Hisbah ya ce ma’auratan sun haɗa da mata 1,500 da maza 1,500 waɗanda za a yi masu gwaje-gwajen lafiya na dole domin tabbatar da yanayin lafiyarsu kafin a ba su damar shiga shirin.
Ƙananan hukumomin da za a gudanar da gwajin sun haɗa da Rogo, Wudil, Tudun Wada, Warawa, Kibiya, Dawakin Tofa, Garun Malam, Kura, da Dambatta.

Source: Original
Sai kuma Karaye, Tsanyawa, Minjibir, Rimin Gado, Shanono, Kabo, Tofa, Rano, Bebeji, Ajingi, Gwarzo, Sumaila, Kiru, Takai da Madobi.
Gwaje-gwajen da za a yi a Kano
Sheikh Aminudeen ya ce hukumar Hisbah ta haɗa kai da ma’aikatar lafiya ta Jihar Kano da kuma hukumar yaƙi da cuta mai karya garkuwar jiki ta jihar domin tabbatar da nasarar aikin.

Kara karanta wannan
Isra'ila ta yi ikirarin hallaka kwamandan Hezbollah ana kokarin tsagaita wuta a Lebanon
Ya bayyana cewa za a yi wa masu gwaje-gwajen cutar HIV/AIDS, amfani da miyagun ƙwayoyi, nau’in jini, ciwon hanta na Hepatitis B da kuma wasu cututtukan da ake kamuwa da su ta hanyar jima’i, daga ciki har da gonoriya.
Mataimakin babban kwamandan ya ce an umarci dukkannin waɗanda suka yi rajista da su garzaya ofisoshin Hisbah da ke ƙananan hukumominsu domin yin gwajin.
Ya yi gargaɗin cewa duk wanda ya kasa bayyana domin yin gwajin za a cire sunansa daga cikin waɗanda za su amfana da shirin.
Ya ce:
“Bayan an kammala hakan, waɗanda suka samu sakamakon gwajin lafiya mai gamsarwa ne kawai za su cancanci shiga shirin."
Za a yi auren gata a Kano
A baya, kun samu labarin cewa rahotanni sun nuna cewa Gwamnatin Kano, karkashin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta shirya gudanar da auren gata a jihar a 2026.
Shugaban hukumar Hisbah na jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya sanar da cewa mutane 3,000 gwamnatin Abba za ta aurar a cikin wannan shekara.
Shugaban hukumar Sheikh Aminu Daurawa ya kuma bayyana abubuwan alheri da gwamnatin Kano ta tanada domin tabbatar da an yi hidimar auren lafiya.
Asali: Legit.ng