Sheikh Aminu Daurawa Ya Jero Darusa 10 ga Kowane Musulmi a Ranar Arafa

Sheikh Aminu Daurawa Ya Jero Darusa 10 ga Kowane Musulmi a Ranar Arafa

  • A yau Talata, 9 ga watan Zul Hijja miliyoyin al'ummar Musulmi da suka samu zuwa aikin Hajji za su gabatar da hawan Arafa a Makkah
  • Malamin addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana wasu muhimman darusa da Musulmi za su koya a ranar
  • Malamin ya ambaci darusan dukufa neman gafarar Allah, yi wa juna afuwa da wasu abubuwa da ya kamata kowane Musulmi ya yi a yau

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Saudi Arabia - Miliyoyin mahajjata a kasar Saudiyya sun fara fita filin Arafa a yau domin gabatar da ibada kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya yi nasiha ga al'ummar Musulmi game da abubuwan da ya kamata su yi a wannan rana mai muhimmanci.

Kara karanta wannan

Hukunce hukuncen dabbobin da ya kamata a yanka domin layya

Sheikh Aminu Daurawa ya yi magana kan hawan Arafa
Masu hawan Arafa a hagu, Sheikh Aminu Daurawa a gefe dama. Hoto: Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa/Getty Images
Source: Facebook

Legit Hausa ta gano cewa Sheikh Daurawa ya fadi darusa 10 da ya kamata kowane Musulmi ya dauka a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Darussa 10 daga ranar Arafa

1. Darasin tuba da komawa ga Allah

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana cewa ranar Arafa rana ce ta gafara da ‘yanta bayi daga wuta zuwa Aljanna.

A kan haka malamin ya yi kira da cewa wannan yana koya wa Musulmi muhimmancin tuba ta gaskiya kafin mutuwa.

2. Darasin haɗin kan Musulmi

Ya bayyana cewa Arafa na haɗa musulmi daga kowane yanki na duniya duk da sabanin harshe da launin fata a wuri guda cikin tufafi iri ɗaya.

Saboda haka ne Sheikh Aminu Daurawa ya ce wannan yana nuna cewa Musulunci addinin haɗin kai ne ba tare da nuna bambanci ba.

3. Darasin tawali’u

Ya ce mahajjata suna tsayuwa cikin ƙasƙantar da kai suna roƙon Allah. Wannan yana koya mana kada girman kai ya shiga zukatanmu.

Kara karanta wannan

Dalilin da ya sa Tinubu ya cancanci 'yan Najeriya su kara ba shi dama a zaben 2027

4. Darasin yawaita addu’a

Daurawa ya ce Ranar Arafa tana daga cikin lokutan da addu’a tafi karɓuwa kuma ake son yawaita addu'a a cikinta.

Babban malamin ya ce yannan yana nuna muhimmancin yawan roƙon Allah a kowane hali mutum ya samu kan shi a ranar Arafa.

5. Darasin tuna ranar ƙiyama

Malamin ya ce taron dubban mutane a Arafa yana tunatar da ranar tashin ƙiyama lokacin da dukkan mutane za su tsaya gaban Allah.

Yadda aka fara hawan Afara a Makka
Wani mahajjaci na addu'a a kan dusten Arafa a Makka. Hoto: Getty mages
Source: Getty Images

6. Darasin hakuri da juriya

Sheikh Daurawa ya bayyana cewa zafin rana, wahala da gajiyar Hajji suna koya wa musulmi hakuri da jurewa domin neman yardar Allah.

7. Darasin yafe wa juna

Ya kara da cewa Arafa rana ce ta rahama da gafara. Don haka ya kamata musulmi ya yafe wa mutane kamar yadda yake son Allah Ya gafarta masa.

8. Darasin amfani da lokaci

Sheikh Aminu Daurawa ya ce ranar Arafa tana koya mana amfani da lokuta masu albarka kafin su wuce, domin rayuwa tana da iyaka.

Kara karanta wannan

Fasto ya taro rigima da Sheikh Jingir kan APC ta ba Musulmi takara a Jos

9. Darasin tsarkake zuciya

A wannan rana mutane suna nisantar saɓo da husuma, suna maida hankali ga ibada. Wannan yana koya mana tsarkake zukata daga hassada da ƙiyayya.

10. Darasin kusanci ga Allah

Malamin ya ce babban manufar Arafa ita ce kusantar Allah ta hanyar zikiri, addu’a da ibada. Wannan yana koya mana cewa farin ciki na gaskiya yana cikin biyayya ga Allah.

Sheikh Daurawa ya kammala da addu'ar cewa:

"Allah ya sa mu kasance cikin waɗanda suke cin moriyar falalar ranar Arafa. Ameen."

Nasiha kan dabbar layya

A wani labarin, mun kawo muku cewa malamin addinin Musulunci, Sheikh Usman Al-Juzuri ya yi nasiha ta musamman game da dabbar layya.

Malamin ya bayyana cewa yana da kyau duk wanda zai yi layya ya tabbata ya nemi dabbar da shari'a ta amince da ita domin samun lada.

Ya yi kira da cewa wajibi be dabbar da za a yanka ta kasance tana da lafiya kuma sai bayan liman ya yi yanka sauran mutane za su fara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng