Mutane Sun Barke da Dariya da Jonathan Ya Kira Sarkin Kano da Wani Suna a cikin Taro
- Mutane sun barke da dariya yayin da tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya kira Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II da abokinsa na kwarai
- Jonathan ya fadi haka ne a wurin taron kaddamar da littafin tarihin rayuwar tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Yakubu Gowon
- Tun a shekarar 2014 aka samu sabani tsakanin Jonathan da Sanusi II lokacin da Sarkin ke kan kujerar gwamnan babban bankin Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya jawo ce-ce-ku-ce bayan ya kira Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, da “abokina na kwarai” a wurin taro.
Rahoto ya nuna cewa mahalarta taron sun barke da dariya lokacin da Jonathan ya kira Sanusi II da abokinsa, saboda ba a yi tsammanin jin haka daga tsohon shugaban kasar ba.

Source: Twitter
Daily Trust ta ruwaito cewa Jonathan ya bayyana hakan ne a taron kaddamar da littafin tarihin rayuwar tsohon shugaban mulkin soja, Janar Yakubu Gowon a Abuja.
An rada wa littafin suna, 'My Life of Duty and Allegiance' kuma an gudanar da taron kaddamar da shi a yau Talata, 19 ga watan Mayu, 2026.
Kalmar da Jontahan ya kira Sanusi II da ita ta sa mahalarta taron fashewa da dariya, lamarin da ya sanya shi dakatawa na dan lokaci kafin ya ci gaba da jawabinsa a matsayin shugaban taron.
Rikicin Jonathan da Sanusi II
A baya, Jonathan da Sarkin Kano na 16 sun samu sabani lokacin da Sanusi yake matsayin gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN).
Rikicin ya samo asali ne bayan zargin da Sanusi ya yi a ranar 13 ga Fabrairu, 2014, a gaban kwamitin kudi na majalisar dattawa cewa kamfanin NNPC bai tura kusan Dala biliyan 20 zuwa baitul-mali ba.
Wannan zargi ya haifar da ce-ce-ku-ce a siyasar Najeriya tare da jawo rashin jituwa tsakanin shugaban kasa da gwamnan CBN a wancan lokaci.
Daga bisani, Jonathan ya dakatar da Sanusi daga mukaminsa na gwamnan CBN, inda ya danganta hakan da zargin rashin da’a da almundahanar kudi.

Source: Facebook
Yadda Sanusi ya zama Sarkin Kano
Bayan dakatar da shi daga CBN, Sanusi ya samu sarautar Sarkin Kano bayan rasuwar marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero, a shekarar 2014.
Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ce ta nada shi, lamarin da ya sake mayar da shi cikin manyan fitattun shugabanni a Najeriya.
Kiran Sanusi II da 'abokina na jwarai' da Jonatahan ya yi a taron ya sa mutane suka yi dariya, amma daga bisani ya karisa jawabinsa, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Jonathan zai fito takara a PDP
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon shugaban kasaGoodluck Jonathan ya shirya tsaf domin fitowa takara karkashin inuwar jam'iyyar PDP a zaben 2027.
Wani rahoto na musamman da aka hada ya nuna cewa Jonathan ya zabi PDP a matsayin jam'iyyar da zai sake neman komawa Aso Rock a zabe na gaba.
Wani babban jami'i a tawagar Jonathan ya tabbatar da hakan a ranar Lahadi, ya ce an dauki wannan matakin ne bayan doguwar tattaunawa.
Asali: Legit.ng

