Wasu ’Yan Bindiga Sun Kashe Jami’an NSCDC 3 da Fararen Hula 2 a Jihar Imo

Wasu ’Yan Bindiga Sun Kashe Jami’an NSCDC 3 da Fararen Hula 2 a Jihar Imo

  • Wasu tsagerun ‘yan ta’adda sun hallaka jami’an tsaro a jihar Imo, lamarin da ya jawo hargitsi a yankin da abin ya faru
  • An ruwaito cewa, baya ga jami’an tsaron, an kashe wasu fararen hula biyu da ke zaune a gefen inda suka farmaka
  • Ya zuwa yanzu dai rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin, amma NSCDC bata ce komai ba

Jihar Imo - Wasu tsagerun ‘yan bindiga a ranar Litinin suka kashe wasu jami’an tsaro uku na hukumar NSCDC da kuma wasu fararen hula biyu a jihar Imo, Punch ta ruwaito.

An ruwaito cewa, ‘yan bindigan sun dura kasuwar Ekelsu ne da ke yankin Obiangwu na karamar hukumar Ngor Okpala ta jihar, inda suka harbe jami’an na NSCDC da mutanen biyu.

Ya zuwa yanzu, rahoto bai bayyana bayanan mutum biyun da aka kashe ba a tare da wadannan jami’an tsaron da ke bakin aiki.

Kara karanta wannan

Abin tausayi: Bayan rikicin zabe, 'yan bindiga sun hallaka 'yan sanda a wata jiha

Yadda 'yan ta'adda suka kashe jami'an tsaro a Imo
Jihar Imo, mai fama da ta'addancin 'yan IPOB | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Yadda lamarin ya faru daga bakin ganau

Wata majiya daga yankin ta bayyana cewa, an farmaki wadannan bayin Allah ne da sanyin safiyar yau Litinin 27 ga watan Maris.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewar majiyar, jami’an na NSCDC na cikin motarsu ne a lokacin da ‘yan ta’addan suka yi musu kwanton bauna tare da kashe su da wasu mutane da ke gefe.

A cewarta, yanzu dai jami’an tsaro sun mamaye yankin tare da kokarin kame duk wasu da ake zargi da aikata barnar a yankin, matasa sun shiga taitayinsu.

Har yanzu ba a tattara gawarwakin ba

Ta kuma kara da cewa, ya zuwa lokacin hada wannan rahoton ba a tattara gawarwakin matattun ba daga inda hakan ya faru.

Sai dai, da aka tuntubi jami’in hulda jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Henry Okoye ya shaidawa The Nation cewa, lamarin ya faru ne da daren jiya Lahadi.

Kara karanta wannan

Kaico: 'Yan ta'adda sun kone wani babban kotu a wata jiha, sun barnata kayan aiki

Kakakin NSCDC, Chimeziri Lowell bai dauki waya ba a lokacin da majiya ta so jin ta bakinsa game da lamarin.

An harbe ‘yan sanda a jihar Enugu

A wani labarin, an naqalto yadda wasu tsagerun ‘yan bindiga suka hallaka jami’an tsaro na ‘yan sanda a jihar Enugu.

Lamarin ya haifar da cece-kuce, inda aka ga gawarwakinjami’an a cikin kwalbatin da ke bakin titi.

Ana yawan samun aukuwar hare-hare kan jami’an tsaro a yankunan kudancin kasar nan, musamman Kudu maso Gabas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.