An Dauke Wutar Lantarki na Awanni 6, TCN Ya Fadi Yankunan da abin Zai Shafa
- Kamfanin TCN ya sanar da daukewar wuta na awa shida a wasu yankunan Osun saboda aikin gyaran na’urar lantarki ranar Alhamis
- Yankunan McPherson, University da Ogunmakin za su kasance cikin duhu daga karfe 10 na safe zuwa 4 na yamma
- TCN ta ce aikin gyaran zai taimaka wajen inganta samar da lantarki da rage matsalolin da ke haddasa daukewar wuta ba zato ba tsammani
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Kamfanin da ke kula da rarraba wutar lantarki na Najeriya (TCN) ya sanar da cewa za a samu daukewar wuta na tsawon awa shida.
TCN, shiyyar Osogbo ya bayyana cewa, yankuna da dama a jihar Osun, za su rasa wutar lantarki a ranar Alhamis, 14 ga Mayun 2026.

Source: Facebook
Dalilin daukewar wutar lantarki a Osun
Kamfanin ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Alhamis, dauke da sa hannun shugabar sashen hulda da jama'a da watsa labarai, Ndidi Mbah.
TCN ya ce za a yi aikin gyaran na’urar lantarki mai karfin 40MVA 132/33KV da ke a karamar tashar rarraba wutar lantarki ta McPherson.
An ce aikin zai gudana daga karfe 10:00 na safe zuwa karfe 4:00 na yamma domin injiniyoyi su gudanar da bincike da gyaran tsarin kariya na yau da kullum.
Kamfanin ya bayyana cewa ana yin aikin ne domin tabbatar da cewa na'urorin sun ci gaba da aiki yadda ya kamata da kuma inganta tsarin samar da lantarki.
Yankunan da abin zai shafa
Sakamakon aikin gyaran, kamfanin da ke rarraba wa yankin Ibadan wuta na IBEDC ba zai iya samar da lantarki ga kwastomominsa a wasu yankuna ba.
Yankunan da za su fuskanci daukewar wutar sun hada da:
- McPherson
- Jami'a
- Ogunmakin

Source: Twitter
TCN ya yi karin haske
Shugaban sashen hulda da jama'a da watsa labarai na TCN, Ndidi Mbah, ta ce aikin gyaran na da muhimmanci wajen rage matsalolin da ka iya haddasa lalacewar wutar lantarki.
A cewarta:
“Ana yin wannan aikin ne domin bai wa ma’aikatan TCN damar gudanar da bincike da gyaran tsarin kariya ga na’urar domin tabbatar da ci gaba da aiki yadda ya kamata.”

Kara karanta wannan
Jonathan ya amsa kiran 'yan Najeriya, zai tsaya takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP
Kamfanin TCN ya kuma nemi afuwar mazauna yankunan da harkokin kasuwanci da abin zai shafa. Kamfanin ya bukaci jama’a su yi hakuri da wannan matsala ta wucin gadi yayin da ake gudanar da aikin gyaran.
Karanta sanarwar a nan kasa:
An daure tsohon ministan lantarki
A wani labari, mun ruwaito cewa, kotu a Abuja ta yanke wa tsohon ministan makamashi, Saleh Mamman hukunci kan zargin badakalar N33.8bn.
Bayanai sun yi nuni da cewa kotun ta yanke masa hukuncin daurin shekaru 75 bisa zargin satar kudaden gwamnati da suka kai kusan N33.8bn.
Alkalin kotu ya ce an tabbatar da laifuffukan damfara da safarar kudi 12 da EFCC ta gabatar, inda aka yanke masa hukunci ba tare da zabin biyan tara ba.
Asali: Legit.ng
