Wasiyya mai ratsa jiki da Gaddafi ya yiwa iyalinsa kafin a kashe shi
A yayin da ya gama tabbatar da cewar bashi da mafita daga dakarun 'yan tawayen NATO da ke kokarin daukan ransa a watan Oktoba na shekarar 2011, Marigayi Gaddafi, tsohon shugaban kasar Libiya, ya bukaci iyalinsa da su yi murnar mutuwar sa - kar su zubar da hawaye.
An kashe marigayi Gaddafi, tsohon shugaban kasar Libiya, a ranar 20 ga watan Oktoba na shekarar 2011, bayan an tunzura jama'ar sun yi masa bore bisa kan cewar yana bautar da su ta hanyar makalewa a kujerar mulki tun shekarar 1969.
Rahotanni sun tabbatar da cewar Gaddafi ya yi ganawar karshe da iyalinsa, kuma ya bar ma su wasiyya mai ratsa jiki.
Ga wasiyyar ta Gaddafi kamar yadda jaridar 'HowAfrica' ta wallafa.
"Ni ne mahaifin ki, Hana. Ke diya ta ce.
"Ni ne mahaifin ki, Aisha. Ke diya ta ce.
"A daren yau zan fita daga maboya ta duk da nasan hakan zai iya kai ni ga rasa raina.
"Kar ku yi kuka ko ku ji bacin ran mutuwa ta, ya ke Hana da Aisha da Safia - ku yi murna.
"Zan mutu a matsayin mumini da kasashe 40 su ka yaka, yaki na zalunci da rashin adalci.
DUBA WANNAN: Kisan dan sanda: An kama tsohon shugaban majalisa da wasu 49
Kasashen yamma da ake zargi da haddasa rikicin kasar Libya ne su ka dauku nauyin sojojin NATO da su ka fake a matsayin 'yan tawaye domin kashe Gaddafi.
Maasana makircin siyasar duniya sun bayyana cewar da gan-gan kasashen su ka shirya kisan Gaddafi ta hanayar fakewa da sojojin tawaye domin sun san cewar za a ga illar kisan Gaddafi a gaba kamar yadda yanzu ta ke faruwa.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng