Nasarawa da Jihohi 2 ne a Sahun Gaba yayin da Za a Fara Kwaso Alhazan Najeriya Yau
- Za a fara dawo da alhazan Najeriya daga kasar Saudiyya zuwa gida a yau Laraba, 3 ga watan Yuni, 2026 bayan kammala ibadar hajji ta bana
- Rahotanni sun nuna cewa alhazan jihar Nasarawa ne za a fara kwasowa daga kasa mai tsarki, sannan sai na jihohin Ogun da Kebbi su biyo baya
- Kamfanin Flynas ya ce ya kammala duk wasu shirye-shirye domin tabbatar da aikin jigilar alhazan ya gudana cikin tsari da aminci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Kamfanin jiragen sama na Flynas ya sanar da cewa za a fara dawo alhazai daga kasar Saudiyya zuwa gida Najeriya daga ranar Laraba, 3 ga Yuni, 2026.
Kamfanin, wanda yana daya daga cikin kamfanonin sufurin jiragen sama da suka yi aikin jigilar alhazan zuwa Saudiyya, ya ce za a fara kawo 'yan jihar Nasarawa zuwa gida a yau.

Source: Twitter
Daily Trust ta ce a cewar sanarwar da kamfanin ya fitar, bayan debo alhazan Nasarawa, alhazan jihohin Ogun da Kebbi ne za su biyo baya a rana ta gaba watau ranar Alhamis, 4 ga Yuni 2026.
Flynas ya tanadi manyan jirage 6
Kamfanin ya bayyana cewa zai gudanar da aikin jigilar dawo da alhazan ne ta amfani da manyan jiragen sama guda shida kirar A330 domin tabbatar da cewa an dawo da su cikin sauki da tsari.
Sanarwar ta ce jirgin da zai dauki rukuni na farko na alhazan jihar Ogun, zai taso daga filin jirgin sama na King Abdulaziz da ke Jeddah zuwa filin jirgin sama na Gateway da ke Abeokuta ranar Alhamis.
Haka kuma, a wannan rana ne za a tashi da rukuni na farko na alhazan jihar Kebbi daga Jeddah zuwa filin jirgin sama na Sir Ahmadu Bello da ke Birnin Kebbi.
Kamfanin ya kara da cewa a ranar 5 ga Yuni, jirage biyu za su sake tasowa daga Jeddah zuwa Abeokuta da Birnin Kebbi domin ci gaba da dawo da sauran alhazan.
An gama shirin dawo da alhazan Najeriya
Shugaban Kamfanin First Planet Travels Limited kuma wakilin Flynas a Najeriya, Alhaji Umar Kaila, ya bayyana cewa an kammala dukkan shirye-shiryen da suka dace domin gudanar da aikin cikin kwarewa da bin ka'idoji.
Alhaji Umar Kaila ya ce a lokacin jigila zuwa Saudiyya, Flynas ya samu nasarar kai maniyyata da jami'ai 11,342 cikin jirage 30 a makonni biyu kacal, lamarin da ya bayyana a matsayin babbar nasara.

Source: Twitter
Ya kuma bayyana cewa kamfanin ya riga ya kawo kwalaben ruwan Zamzam guda 13,832 na lita biyar-biyar zuwa Najeriya kafin fara dawowar alhazan, innji rahoton Channels tv.
A cewarsa, kamfanin Flynas zai dauki nauyin dawo da alhazan Najeriya da suka fito daga jihohin Kebbi, Lagos, Osun, Kaduna, Neja, Ogun da Nasarawa.
An samu karin alhazai a hajjin 2026
A wani rahoton, kun ji cewa hukumar ƙididdiga ta Saudiyya ta sanar da cewa mahajjata miliyan 1.7 ne suka gudanar da aikin Hajjin 2026.
Alƙaluman da aka fitar bayan kammala aikin Hajjin shekarar 1447AH sun nuna ƙarin alhazai idan aka kwatanta da bara da aka samu mutum 1,673,230.
Hukumar ta bayyana cewa kididdigar ta ƙunshi dukkan maza da mata da suka halarci aikin Hajjin bana a birnin Makkah da sauran wurare masu tsarki.
Asali: Legit.ng


