Dama ta samu: An sake buɗe shafin bada tallafin rancen COVID-19 daga bankin CBN

Dama ta samu: An sake buɗe shafin bada tallafin rancen COVID-19 daga bankin CBN

- Babban bankin Nigeria, CBN, ya sake bude shirin bada rance ga jama'a da annobar korona ta yi wa tattalin arzikinsu illa

- Wannan dai shine karo na biyu da CBN ke bada rancen ta hannun bankin manoma NIRSAL ga yan Nigeria

- Sanarwar ta NIRSAL ta fitar ya ce magidanta na iya karba har zuwa naira miliyan 3 yayin da kananan masana'antu na iya karba zuwa naira miliyan 25

Babban bankin Nigeria, CBN, ta sake bude shafinta na TCF don bada rance ga wadanda suka fada matsin tattalin arziki sakamakon annobar COVID-19.

Bankin bada bashi ga manoma ta NIRSAL ne ta sanar da hakan a ranar Litinin cikin wani sako da ta wallafa a Twitter.

An sake buɗe shafin bada rancen COVID-19 daga bankin CBN
An sake buɗe shafin bada rancen COVID-19 daga bankin CBN. Hoto: @PremiumTimesNG
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Matawalle ya bawa ƴan bindiga wa'addin watanni biyu su tuba su miƙa makamansu

CBN ta bullo da tsarin ne domin tallafawa jama'a, masu kananan sana'o'i da matsakaitan kamfanoni su farfado daga illar da annobar korona ta yi musu. Bankin NIRSAL ne ke da hakkin rabar da bashin.

Wannan shine karo na biyu da gwamnati ke bada bashin, an bada karo na farko ne tun daga watan Maris na 2020.

A cewar NIRSAL, a kalla mutane 3,256 of 80,000 da suka kunshi magidanta, masu kananan sana'o'i da matsakaitan kamfanoni ne suka amfana da bashin har zuwa Afrilun 2020.

KU KARANTA: Kotu ta raba aure saboda mata da yara suna lakaɗawa maigida duka

Za a bada bashin ne kan kudin ruwa 9% duk shekara na adadin kudin da mutum ya karba.

Bankin na CBN ta sanar a makon da ta gabata cewa wadanda suka karbi bashin a baya za su biya ruwa na 5% ne har zuwa 2022.

Za a biya bashin ne a kasa da shekaru uku.

Magidanta za su iya karbar har zuwa naira miliyan 3, kananan kamfanoni kuma za su iya karba har zuwa naira miliyan 25 duk da cewa hakan ya danganta da yanayin kudin da kamfanin ke juyawa.

A wani rahoton daban kun ji cewa, rundunar yan sandan jihar Kano ta kwantar da jama'a hankula game da wasu bakin mutane tare da rakuma da suka bayyana a wasu sassan jihar.

Daily Nigerian ta gano cewa mazauna jihar sun ankarar da yan sanda kan bakin mutanen da suka yada zango a wasu sassan jihar.

Wasu mazauna garin suna zargin matafiyar sun iso jihar ne domin aikata laifi da sunan fataucin kanwa.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164