Saudiyya: Dole ne duk wanda zai zo aikin Hajji yayi allurar rigakafin COVID-19

Saudiyya: Dole ne duk wanda zai zo aikin Hajji yayi allurar rigakafin COVID-19

- Kasar Saudiyya ta bayyana cewa, dole ne dukkan masu zuwa Hajjin bana su yi rigakafin Korona

- Kasar tace allurar rigakafin zata zama daya daga cikin sharruddan shiga kasar ta Saudiyya

- Hakazalika kasar ta bayyana shirinta na tabbatar da gudanar da aikin Hajjin bana, 2021

Masarautar Saudiyya ta umarci maniyyata da su yi allurar rigakafin COVID-19 gabanin aikin Hajjin na 2021, in ji jaridar Okaz.

Masarautar ta bakin Ministan Kiwon Lafiya, Tawfiq al-Rabiah, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Litinin din da ta gabata, Aljazeera ta ruwaito.

Ministan ya ce "Alurar rigakafin ta COVID-19 wajibi ne ga wadanda suke son zuwa aikin Hajji kuma zai kasance daya daga cikin manyan sharudda (na karbar izinin zuwa)."

Aikin Hajji shiri ne na hajji wanda ke maraba da miliyoyin Musulmai a duk faɗin duniya wadanda yawanci sukan ziyarci Ka’aba, “Dakin Allah” a cikin garin Makka mai alfarma, a Masarautar Saudiyya.

KU KARANTA: APC ba zata taba iya cire 'yan Najeriya daga kangin da suke ciki ba, in ji Saraki

Saudiyya: Dole ne duk wanda zai zo aikin Hajji yayi allurar rigakafin COVID-19
Saudiyya: Dole ne duk wanda zai zo aikin Hajji yayi allurar rigakafin COVID-19 Hoto: BBC
Asali: UGC

Har ila yau, shirin ya kasance wani karin hanyar samun kudin shiga ga kasar ta Gabas ta Tsakiya mai arzikin mai.

A shekarar 2019, shirin aikin hajji ya samu sama da baki miliyan biyu a duk fadin duniya. Aikin hajji, duk da haka, ya sami babbar matsala a shekarar 2020 saboda bullowar COVID-19 kamar yadda ibadar ta kasance iyakance ga mutane 10,000 kadai.

Mummunar cutar ta kashe sama da mutane miliyan biyu a duniya kuma ta kuma harbu mutane miliyan 115 da aka tabbatar da cutar tun barkewarta a Wuhan ta kasar China a shekarar 2019.

Wasu manyan kamfanonin harhada magunguna sun kera alluran rigakafi game da mummunar cutar, yayin da rarraba alluran ke gudana a duk fadin duniya.

KU KARANTA: Makinde: Ba za mu bada filayen kiwo ga makiyaya kyauta ba, dole su biya

A wani labarin, Allurar rigakafin Oxford-AstraZeneca da NAFDAC ta amince dasu sun iso kasar Najeriya da tsakar ranar Talata, a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja, ta wani kamfanin jirgin sama na Emirates, Channels Tv ta ruwaito.

Shugaban kwamitin tsaro na shugaban kasa (PTF) kan COVID-19, Boss Mustapha, ya fada a ranar Asabar cewa Najeriya za ta karbi kaso na farko na kimanin allurai miliyan 4 na COVID-19.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel