Zargin Daukar Nauyin Ta'addanci: Kotu Ta Yi Hukunci Kan Bukatar Tukur Mamu

Zargin Daukar Nauyin Ta'addanci: Kotu Ta Yi Hukunci Kan Bukatar Tukur Mamu

  • Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta ƙi amincewa da buƙatar da Tukur Mamu ya yi na a mayar da shi gidan gyaran hali na Kuje
  • Mai shari'a Inyang Ekwo shi ne ya yi fatali da buƙatar Tukur Mamu wanda gwamnatin tarayya ke zargi da ɗaukar nauyin ta'addanci
  • Sai dai, mai shari'ar ya umarci hukumar ƴan sandan farin kaya ta DSS da ta riƙa bari yana ganin likitansa domin duba lafiyarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Mai shari’a Inyang Ekwo na babbar kotun tarayya da ke Abuja, ya yi watsi da buƙatar Mohammed Tukur Mamu.

Tukur Mamu wanda ake zargi da ɗaukar nauyin ta'addanci ya buƙaci a ɗauke shi daga hannun hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) zuwa gidan gyaran hali na Kuje.

Kara karanta wannan

Goodluck Jonathan ya tsoma baki kan rigimar Ministan Tinubu da gwamnan PDP

Kotu ta yi fatali da bukatar Tukur Mamu
Kotu ta ki yarda a mayar da Tukur Mamu gidan gyaran hali na Kuje Hoto: MadukaOgwueleka
Asali: Facebook

Da yake yanke hukuncin a ranar Litinin, Mai shari’a Ekwo ya ce gwamnatin tarayya ta taɓo batun fasa gidajen yari a matsayin babban dalilin adawa da buƙatar mayar da shi zuwa Kuje, cewar rahoton tashar Channels tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin watsi da bukatar Tukur Mamu?

Alƙalin ya kara da cewa, Mamu bai yi adawa da batun da gwamnatin tarayyar ta kawo ba kan fasa gidajen yarin kamar yadda doka ta tanada.

A cewar mai shari’a Inyang Ekwo, tunda Mamu bai ƙalubalanci hakan ba, hakan ya nuna cewa ya amince da batun kuma babu buƙatar ƙarin wata hujja, rahoton jaridar TheCable ya tabbatar.

Daga nan ne alƙalin ya umarci Tukur Mamu da ya ci gaba da zama a hannun DSS a duk tsawon lokacin da za a kwashe kan shari’ar da ake yi masa.

Kara karanta wannan

"Mu taimaka masu," Ganduje ya yi magana kan mummunan harin da aka kai Masallaci a Kano

Sai dai mai shari’a Inyang Ekwo, ya tabbatar da umarnin da ya bayar a baya cewa a bar shi ya je wurin likitansa domin duba lafiyarsa tare da kulawar hukumar DSS.

Daga nan sai ya sanya ranakun 3, 4, 5 da 6 na watan Yunin 2024 domin ci gaba da sauraron shari'ar.

Tukur Mamu ya ɗauki zafi

A wani labarin kuma, kun ji cewa Tukur Mamu ya bukaci ministan shari'a na Najeriya da ya janye zargin da gwamnatin tarayya ke yi kansa na ɗaukar nauyin ta'addanci.

Tukur Mamu ya ba da wa'adin kwanaki bakwai tare da shan alwashin ɗaukar mataki idan har ba a cire sunansa daga cikin waɗanda ake zargi da daukar nauyin taaddanci ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng