Janar Tsiga: Yadda 'Yan Bindiga Suka Shammaci Jama'a Suka Sace Tsohon Shugaban NYSC
- Majiyoyi sun bayyana yadda ƴan bindiga suka sace tsohon shugaban hukumar kula da masu yi wa ƙasa hidima (NYSC)
- An bayyana cewa ƴan bindigan sun sauya salo lokacin da suka je sace Janar Maharazu Tsiga a gidansa da ke jihar Katsina
- Wata majiya ta ce har mutanen da ke wajen wani mai shayi ba su fahimci abin da ya faru ba, sai bayan an sace tsohon sojan
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - An samu ƙarin bayanai kan yadda ƴan bindiga suka sace tsohon shugaban hukumar NYSC, Birgediya Janar Maharazu Tsiga (mai ritaya) a jihar Katsina.
Rahotanni sun nuna cewa ƴan bindigan sun sauya dabarunsu wajen yin garkuwa da Birgediya-Janar Maharazu Tsiga, a gidansa a makon da ya gabata.

Asali: Facebook
Ƴan bindiga sun sauya salo wajen sace Janar Tsiga

Kara karanta wannan
Katsina: Likitan da ke kula da lafiyar 'yan ta'adda ya shiga hannun jami'an tsaro
Jaridar Leadership ta ce wata majiya ta bayyana cewa ƴan bindigan sun aiwatar da shirin nasu ne cikin tsanaki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyar ta ce ƴan bindigan ba su yarda sun yi arangama da jami’an tsaro ko ƙungiyoyin ƴan sa-kai ba, kafin su sace Birgediya-Janar Maharazu Tsiga ba.
Wannan sabon salo ya biyo bayan yadda al’ummomi ke ci gaba da kafa ƙungiyoyin ƴan banga domin kare kansu daga hare-haren ƴan bindiga.
Yadda aka sace tsohon shugaban NYSC
Wani mazaunin yankin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana takaicinsa kan yadda aka sace tsohon shugaban na hukumar NYSC cikin sauƙi.
Duk da cewa tsohon jami’in soja ne wanda ya samu horo kuma yana da makami a tare da shi, Birgediya Janar Tsiga bai yi musu turjiya ba.
“Birgediya Janar Maharazu Tsiga ne da kansa ya buɗe musu ƙofa, suka gaisa, sannan suka ce masa, ‘mun zo ɗaukarka.’ Har ma ya nemi izinin ɗaukar hularsa kafin ya bi su."
"Da ace ya yi harbi ko sau ɗaya, ƴan rundunar tsaron Radda da ƙungiyoyin sa-kai da ke kusa za su yi gaggawar ɗaukar mataki."
- Wata majiya
Sai dai, ƴan bindigan sun yi garkuwa da tsohon shugaban na NYSC ne a cikin tsanaki sosai, ta yadda har mutanen da ke kusa da wani shagon shayi ba su fahimci abin da ke faruwa ba.
Sojoji na ƙoƙarin ceto tsohon sojan
Bayan sace shi, rundunar sojojin Najeriya ta ƙaddamar da farmaki mai ƙarfi kan waɗanda suka sace shi, inda ta hana su ƙoƙarin fitar da Birgediya Janar Tsiga daga Najeriya.
Rahotanni sun nuna cewa jami’an tsaro sun kulle duk wata hanya da ƴan bindigan za su iya tserewa, kuma suna ci gaba da ƙoƙarin ceto shi.
Duk da cewa hukumomi ba su fitar da wata sanarwa ba tukuna, rahotanni sun bayyana cewa ƴn bindigan na bukatar kudin fansa har Naira miliyan 250 daga iyalansa domin su sake shi.
Su wanene masu hannu a sace Janar Tsiga?
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙaramar hukumar Bakori, ya yi magana kan masu hannu a sace Birgediya-Janar Maharazu Tsiga.
Honarabul Ali Mamman Mai Chitta ya bayyana cewa masu ba ƴan bindiga bayanai ne suka yi silar sace tsohon shugaban na hukumar NYSC.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng