Faretin Isra'ila: Zohran Mamdani Ya Kauracewa Babban Taron Yahudawa a Amurka

Faretin Isra'ila: Zohran Mamdani Ya Kauracewa Babban Taron Yahudawa a Amurka

  • Magajin garin New York, Zohran Mamdani ya tabbatar cewa ba zai halarci bikin shekara-shekara na Yahuwadan Isra'ila da za a gudanar a ranar Lahadi ba
  • Rahotanni sun bayyana cewa hakan ya sanya Zohran Mamdani ya zama magajin garin New York na farko da ba zai halarci taron ba tun shekarar 1964
  • A cikin shekaru 61 da suka gabata, kowane magajin garin da ke kan mulki a birnin New York City ya kasance yana halartar faretin da Yahudawa ke yi a Amurka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - Magajin garin New York, Zohran Mamdani ba zai halarci bikin shekara-shekara na Yahudawa da za a gudanar a birninsa ranar Lahadi mai zuwa ba.

Hakan ya sanya ya saba wata tsohuwar al’ada da ta shafe shekaru da dama, duk da cewa yana halartar wasu bukukuwa da ke nuna bambancin al’adun birnin.

Kara karanta wannan

'Jirgi marar matuki zan nada': Sowore kan wanda zai ba ministan tsaro idan ya ci mulki

Zohran Mamdani
Magajin garin New York, Zohran Mamdani. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Jerussalem Post ta ce tun daga shekarar 1964, kowane magajin garin da ke kan mulki a New York City ya kasance yana halartar wannan biki na Yahudawa.

Dalilin Zohran Mamdani na kin zuwa taron

Wani rahoto da Fox News ta wallafa ya nuna cewa Mamdani ya bayyana cewa rashin halartarsa taron ya samo asali ne daga matsaya ta siyasa.

Ya sha sukar Isra’ila akai-akai bayan harin Hamas na 7 ga Oktoba, 2023, kuma bayan hawa kujerar mulki a watan Janairun 2026, ya soke wata doka da ta hana hukumomin birnin tsoma baki a yakin.

Mai magana da yawunsa ya shaida cewa ya ce:

“Duk da cewa ba zan halarci taron Yahudawa ba, bai kamata a dauki rashin halartata a matsayin kin bayar da tsaro ko lasisin da ake bukata don tsaron taron ba.
"Na bayyana a fili: na yi imani da daidaiton hakkoki ga kowa a ko’ina. Wannan ka’ida ce da nake bi a ko da yaushe.”

Kara karanta wannan

Ayyukan da Tinubu ya saka a gaba bayan gwamnatinsa ta shekara 3 a mulkin Najeriya

Zohran Mamdani a New York
Lokacin da Zohran Mamdani ya yi rantsuwar fara aiki a New York. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Mamdani ya halarci wasu bukukuwa a New York

Duk da matsayarsa kan Isra’ila, magajin garin ya halarci wasu bukukuwa, ciki har da bikin St. Patrick’s Day na bana, inda ya kwatanta halin da Irish suka fuskanta a tarihi da kisan kare dangi a Falasdinu a lokacin yakin Isra’ila da Hamas.

A bikin sabuwar shekara ta Lunar da aka yi a watan Maris, 2026 a birnin New York, Mamdani ya halarci taron tare da Gwamna Kathy Hochul.

A watan Yunin 2026, New York za ta karbi bakuncin babban bikin Puerto, daya daga cikin manyan bukukuwa a birnin. Ko da yake bai tabbatar ko zai halarta ba a bana, yana da tarihin shiga irin wannan bukukuwa.

Netanyahu ya yi waya da Trump

A wani labarin, mun kawo muku cewa Firaministan Isra'ila ya yi magana da shugaban Amurka, Donald Trump ta wayar tarho.

Netanyahu ya tattauna da Trump ne a kan wasu abubuwa da suka shafi yakin da Amurka da Isra'ila suka kaddamar a kan Iran.

Maganar da shugabannin suka yi tazo ne a daidai lokacin da Amurka da Iran ke kai wa juna hari duk da batun tsagaita wuta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng