'Yan Bindiga Sun Yi Tsaurin Ido, Sun Yi Garkuwa da Birgediya Janar Maharazu Tsiga
- Ƴan bindiga sun shiga garin Tsiga, ƙaramar hukumar Bakori a Katsina, sun yi garkuwa da tsohon Darakta Janar na NYSC, Maharazu Tsiga
- An tattaro cewa ƴan ta'addar sun afka garin ne da tsakar dare misalin ƙarfe 12:30, sun ɗauki mutane da dama har da Janar Tsiga mai ritaya
- 'Dan majalisar Bakori da Ɗanja, Hon. Abdullahi Balarabe Dabai ya tabbatar da lamarin, ya miƙa jaje ga al'ummar yankin da Katsina baki ɗaya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Katsina - A wani al’amari mai ban tsoro, ‘yan bindiga sun kai mummunan hari a garin Tsiga da ke ƙaramar hukumar Bakori a jihar Katsina
Ƴan bindigar ɗauke da mugayen makamai sun yi garkuwa da muatane da dama, ciki har da tsohon shugaban hukumar kula da ƴan bautar ƙasa (NYSC), Manjo Janar Maharazu Tsiga (mai ritaya).

Asali: Facebook
Jaridar Leadership ta tattaro cewa harin ya faru ne da sanyin safiyar Alhamis, da misalin ƙarfe 12:30 na tsakar dare lokacin da ‘yan bindigar suka afka yankin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan bindiga sun firgita mutane a harin Bakori
Harin ƴan ta'addan da sace babban mutum irin Maharazu Tsiga ya haifar da firgici da tashin hankali ga mazauna yankin gaba ɗaya.
Wasu da suka san yadda harin ya afku sun bayyana cewa tuni aka sanar da hukumomin da abin ya shafa kuma jami’an tsaro suna aiki tukuru domin ceto waɗanda aka sace.
Har zuwa lokacin da ake tattara wannan rahoto, babu wasu cikakkun bayanai kan adadin sauran mutanen da suka fada hannun ‘yan bindigar.
Ɗan Majalisar Bakori/Ɗanja ya tabbatar da harin
Ɗan majalisar wakilan tarayya mai wakiltar Bakori da Ɗanja, Hon. Abdullahi Balarabe Dabai ya tabbatar da aukuwar wannan lamarin a shafin Facebook.
"Innalillahi wa inna Ilahirrajiun, na samu labari mara dadi na mummunan harin da yan bindiga suka kai garin Tsiga, ƙaramar hukumar Bakori a daren jiya Laraba ga watan Fabrairu, 2025.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun yi ta'adi, an gano gawar ɗan Majalisar da suka sace a wani yanayi
"Sun yi garkuwa da mutane biyu daga ciki akwai matashi daya da Dattijo Birgediya Janar Maharazu Ismail Tsiga (mai ritaya), tsohon Darakta Janar na NYSC."
Wannan ba ƙaramar barazana ba ce gare mu, ina mika sakon jajena ga dukkanin al'ummar wannan yanki da karamar hukumar Bakori da jihar Katsina baki daya. Za mu yi bakin ƙoƙarin wajen magance lamarin In sha Allahu.
- Hon. Abdullahi Balarabe.
Yadda aka sace Janar Maharazu Tsiga
Wani mazaunin Tsiga, Abdullahi Tsiga ya shaidawa wakilin Legit Hausa ta wayar tarho cewa maharan sun shiga garin ne da daddare kuma sun yi ɓarna.
"Mun wayi gari ne da wannan mummunan labarin, sun shigo da tsakar dare duk da ba wani dare ne can-can ba, misalin karfe 12:30 haka, sun yi ɓarna sun fasa abubuwa.
"Mun samu labarin sun ƙara ɗaukar mutane a kauyuka haka bayan sun bar nan. Har yanzu ba su kira kowa ba, yanzu haka ina gidan Maharazu Tsiga," in ji shi.
Yan bindiga sun sace sarki a Edo
A wani labarin, kun ji cewa ƴan bindiga sun yi garkuwa da basarake tare da wasu mutane a jihar Edo da ke Kudancin Najeriya.
Ƴan bindigar sun buɗe wuta bayan sun tare basaraken, suka bindige wani ɗan acaba har lahira kafin su tafi da sarkin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng