Matatar Dangote Ta Sauya Farashin Man Fetur, An Samu Karin N75 kan Kowace Lita

Matatar Dangote Ta Sauya Farashin Man Fetur, An Samu Karin N75 kan Kowace Lita

  • Matatar man Dangote ta sake sauya farashin man farashin fetur, inda ta ƙara kuɗin da take sayar wa ƴan kasuwa litar man zuwa N1,350
  • Sabon sauyin ya nuna ƙarin N75 daga N1,275 da aka sayar a baya, wanda ke zama ƙari na biyu da aka samu na N75 a cikin kwanaki bakwai kacal
  • Sauyin farashin fetur da matatar Dangote ta yi yana zuwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar matsin lamba a kasuwar danyen mai ta duniya

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Legas - Matatar man Dangote ta sake yin wani garambawul ga farashin fetur, inda ta ƙara kudin da take sayar wa 'yan kasuwa litar man zuwa N1,350 a ma'ajiyar ta.

Sabon sauyin da aka samu na ƙarin N75 daga N1,275 da matatar ta sayar da kowace lita a baya, ya nuna yadda ake samun canjin farashi akai-akai a makwannin nan.

Kara karanta wannan

Bayan abin da ya faru, an haramta wa masu digirin girmamawa amfani da 'Dr' a Najeriya

Matatar Dangote ta sauya farashin litar fetur
Ma'aikaci na sayar da fetur a gidan mai. Hoto: Bloomberg / Getty Images
Source: Getty Images

Dangote ya kara farashin man fetur

Legit Hausa ta ci karo da wannan sauyin ne a wani rahoto da shafin Petroleumprice.ng ya fitar a ranar Laraba, 6 ga watan Mayun 2026.

Wata majiya ta shaida cewa an riga an fara amfani da sabon farashin a dukkan wuraren loda mai, wanda hakan ya tilasta wa masu sayar da mai canza farashi litar a gidajensu mansu nan take.

Wani babban jami'i daga matatar wanda ke da masaniya kan wannan lamari ya ce:

"An riga an sauya sabon farashin farashin a ko'ina. An sabunta dukkan wuraren loda mai, kuma tuni masu sayar da mai suka fara daidaita farashin su tun daga rumbunan ajiyarsu zuwa gidajen mai."

Wannan ƙarin farashin na zuwa ne kusan mako guda bayan da Matatar Dangote ta ƙara farashin ta daga N1,200 zuwa N1,275.

Wannan kuma shi ne karo na biyu da aka samu ƙarin N75 a cikin kwanaki bakwai.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai harin ramuwar gayya a Katsina, an kashe bayin Allah

Wasu dalilai na karin kudin man fetur

Duk da waɗannan sauye-sauyen farashin, wani babban jami'in gudanarwa na rukunin kamfanonin Dangote ya bayyana cewa matatar man Dangote tana bayar da tallafi a kan man fetur da dizal da take sayarwa a kasuwar Najeriya.

Hakazalika, an ce ƙarin nan na zuwa ne a yayin da aka dakatar da bayar da takardun biyan kuɗi na 'PFI' a farkon wannan makon.

Jaridar Punch ta rahoto cewa 'yan kasuwa sun yi korafi da cewa ya ƙara taƙaita samun mai sannan ya rura wutar ƙarin farashi a dukkan sassan kasuwancin mai.

"Dakatar da takardun PFI ya haifar da ƙarancin mai na ɗan lokaci," in ji jami'in.

Ya kara da cewa:

"Idan aka haɗa wannan da yadda farashin danyen mai ke tashi a duniya da kuma kuɗin sufuri, ya zama dole farashin ya ƙaru. Abin da muke gani martani ne kai tsaye na kasuwa ga waɗannan matsalolin."
Matatar Dangote ta kara kudin fetur yayin da ake samu sauyin farashin ganganar danyen mai
Alhaji Aliko Dangote da hoton wani bangare na matatar mansa da ke Legas. Hoto: Bloomberg/Contributor
Source: Getty Images

Farashin danyen mai a kasuwannin duniya

Kara karanta wannan

NLC, TUC sun tsayar da lokacin tattauna sabon mafi ƙarancin albashi da gwamnatin Najeriya

Wannan ƙarin na N75 yana zuwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar matsin lamba a kasuwar mai ta duniya da kuma sauye-sauye a hanyoyin rarraba mai a cikin gida, in ji rahoton Channels TV.

Farashin mai ya faɗi da kusan 4/100% a ranar Talata, sannan a ranar Laraba ya ci gaba da faɗuwa, inda danyen man nan na West Texas Intermediate (WTI) ya ɗan sauka ƙasa da dala 100 a kowace ganga.

Dangote ya ba surukinsa mukami

A wani labari, mun ruwaito cewa, an naɗa Jamil Mohammed Abubakar a matsayin shugaban sashen kayayyakin more rayuwa da sufuri a kamfanin Dangote.

Jamil Mohammed Abubakar, surukin Aliko Dangote ne kuma naɗin na zuwa ne a cikin wani tsari na mika ragamar shugabanci ga ‘yan gida.

Ana sa ran zai jagoranci faɗaɗa ayyukan tashoshin jiragen ruwa da hanyoyin kasuwanci a Najeriya da sauran ƙasashen nahiyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com