Wata Sabuwa: Trump zai Kawo Sabon Kudi Mai Dauke da Hoton Shi a Amurka

Wata Sabuwa: Trump zai Kawo Sabon Kudi Mai Dauke da Hoton Shi a Amurka

  • Hukumar buga kudi ta Amurka na duba yiwuwar buga takardar Dala 250 mai dauke da hoton shugaba Donald Trump domin bikin cika shekaru 250 da kafa kasar
  • Idan shirin ya tabbata, wannan zai kasance karo na farko cikin fiye da shekaru 150 da za a saka hoton mutumin da ya ke raye a kudin kasar Amurka
  • Rahotanni da suka fito daga daga kasar sun suna cewa wani kakakin baitulmalin kasar ya tabbatar da shirin da ake yi tare yin karin haske game da halin da ake ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - Sakataren Baitulmalin Amurka, Scott Bessent, ya ce fadar White House na matsa wa majalisae kasar ta amince da sabon kudi, wanda hakan zai bukaci sauya tsohuwar dokar tarayya da ta hana saka hoton mutum mai rai.

Kara karanta wannan

Faretin Isra'ila: Zohran Mamdani ya kauracewa babban taron Yahudawa a Amurka

Hakan na zuwa ne yayin da aka fara maganar saka hoton shugaba Donald Trump a kudin Amurka, duk da cewa yana raye a duniya.

Scott Bessent a fadar White House
Scott Bessent dauke da samfurin dalar Amurka mai hoton Donald Trump. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Batun saka hoton Donald Trump a kudi

Rahoton the Gurdian ya nuna cewa Bessent ya ce sabon kudin zai kasance ne domin bikin cika shekaru 250 da samun ’yancin kan Amurka, kuma baitul-malin ya fara shirye-shiryen yiwuwar samar da kudin.

“A matsayina na shugaban Baitul-malin Amurka, akwai sharuda biyu da suka shafi kudin Amurka a yanzu: babu wani mutum mai rai da zai kasance a jikin kudin Amurka, sannan kudin dole ne ya kunshi kalmar ‘In God we trust’,”

In ji Bessent.

“Saboda haka, yanzu akwai kudirin doka a gaban majalisar wakilai da kuma majalisar dattawa domin sauya sharadi na farko, ta yadda mutum mai rai – Donald J Trump – zai iya kasancewa a jikin takardar kudin dala 250.”

Jaridar Washington Post ta rawaito cewa wasu jami’an baitulmalin guda biyu da Trump ya nada sun matsa wa ma’aikata su fara shirya samfurin takardar kudin, lamarin da ya jawo damuwa cewa hakan zai iya karya dokar kasar.

Kara karanta wannan

Ana tsoron bullar cutar Ebola mai hadari a Kano, Borno da wasu jihohin Najeriya

Za a bi doka wajen buga dalar Amurka

Sai dai duk da matsin lambar da ake yi, wani rahoto ya nuna cewa Bessent ya ce ma’aikatar baitul-malin za ta bi doka, yana mai cewa komai zai tafi a kan tsari.

Mutumin da ya tsara samfurin kudin wani dan Birtaniya ne mai suna Iain Alexander, wanda ya bayyana kansa a yanar gizo a matsayin mai zana hotunan sarauta, mai sassaka mutum-mutumi.

Bessent ya kare sabon kudin lokacin da wani dan jarida ya tambaye shi ko ya dace a sanya hoton Trump a takardar kudi yayin da Amurkawa da dama ke fama da tsadar rayuwa da wahalar sayen kayan yau da kullum.

Bessent ya ce babu wani abu mara dacewa wajen saka shugaban da ke mulki a lokacin bikin cika shekaru 250 da kafuwar kasar a jikin kudi.

Shugaba Donald Trump
Shugaba Donald Trump yana wani bayani a Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

An harbo jirgin Amurka a Iran

A wani labarin, mun kawo muku cewa Gwamnatin Iran ta sanar da cewa ta harbo wani jirgin kasar Amurka da ya shiga sararin samaniyarta.

Kara karanta wannan

Ayyukan da Tinubu ya saka a gaba bayan gwamnatinsa ta shekara 3 a mulkin Najeriya

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake cigaba da samun sabani da kai hare-hare tsakanin Amurka da Iran a Gabas ta Tsakiya.

Biyo bayan maganar Iran, rundunar sojin Amurka ta ce babu kamshin gaskiya a cikin labarin, inda ta ce babu wani jirginta da aka harbo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng