Hajjin 2026: Gwamnan Sokoto Ya Gwangwaje Mahajjata da Kyautar Sallah
- Mahajjatan jihar Sokoto da ke gudanar da ke gudanar da aikin Hajji a Saudiyya sun samu kyautar kudi daga wajen Gwamna Ahmed Aliyu
- Gwamna Ahmed Aliyu ya ba da kyautar kudi ga mahajjatan wadanda ke gudanar da aikin ibada a kasa mai tsarki
- Amirul Hajji na Sokoto ya yaba da halayen da mahajjatan suka nuna a Saudiyya inda ya bukaci su yi addu'o'in samun zaman lafiya a jihar da Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Birnin Makka, Saudiyya - Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya ba da gudunmawar Riyal 1,000 na ƙasar Saudiyya ga mahajjatan jihar da ke Saudiyya.
Gwamna Ahmed Aliyu ya ba da kudin wadanda suka yi daidai da kusan naira 450,000, ga kowane daga cikin mahajjata 2,410 daga jihar da a halin yanzu suke gudanar da aikin hajjin shekarar 2026 a ƙasar Saudiyya.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ce an sanar da wannan gudunmawa ne a yammacin ranar Alhamis, 28 ga watan Mayun 2026 a Mina.
Gwamna Aliyu ya ba mahajjata kyautar kudi
Amirul Hajj na jihar Sokoto kuma Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Alhaji Muhammad Mai Gari Dingyadi, ya sanar da hakan lokacin da yake jawabi ga mahajjatan.
Dingyadi ya bayyana wannan mataki a matsayin kyautar Sallah daga gwamnan da nufin samar da tallafin kuɗi ga mahajjatan yayin da suke shirin komawa gida Najeriya bayan kammala ibadar aikin hajji.
An yabawa mahajjatan Sokoto
Ya yaba da halayen mahajjatan na Sokoto a duk tsawon zamansu a kasa mai tsarki, inda ya nuna gamsuwa da cewa ba a samu kowannensu da laifin keta dokokin ƙasar Saudiyya ba, jaridar The Punch ta kawo labarin.
A cewarsa, irin halayen koyi da mahajjatan suka nuna ya fitar da kyakkyawan hoto na jihar Sokoto da kuma Najeriya baki ɗaya.
“Ina matuƙar farin ciki da irin ladabi, juriya, da kyakkyawan hali da mahajjatanmu suka nuna a lokacin aikin hajjin wannan shekara."
- Mohammed Mai Gari Dingyadi
Ya buƙaci mahajjatan da su dore da wannan tsari na biyayya da sauke nauyi, inda ya lura cewa sun kasance jakadu na gari masu daraja ga jihar.

Source: Facebook
An bukaci mahajjata su yi addu'a
Haka zalika, Amirul Hajj ya sake tabbatar wa mahajjatan irin jajircewar da gwamnatin Gwamna Ahmed Aliyu ke da shi na ci gaba da kula da walwalar al'ummar jihar Sokoto.
Ya yi kira ga mahajjatan da su ci gaba da yin addu'o'in samun nasarar gwamnati mai ci a yanzu, da kuma dorewar zaman lafiya da tsaro a jihar Sokoto da kuma faɗin Najeriya baki ɗaya.
Dingyadi ya yi roƙo na musamman ga mahajjatan da su roƙi Allah da gaske domin kawo ƙarshen rashin tsaro da sauran ƙalubalen da ke addabar ƙasar.
Saudiyya ta gargadi mahajjata
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumomi a Saudiyya sun gargadi mahajjatan da ke gudanar da aikin hajjin shekarar 2026.
Hukumar kula da yanayi ta Saudiyya ta gargadi mahajjata da su shirya wa matsanancin yanayin zafi, inda ake sa ran yanayin zafin zai tashi har zuwa digiri 47 na ma'aunin Celsius a lokacin gudanar da aikin hajjin.
Hakazalika, hukumar ta buƙaci mahajjata da su ɗauki matakan kariya domin kauce wa rukunonin cututtuka da zafi ke haifarwa.
Asali: Legit.ng


