"A Kula": Saudiyya Ta Gargadi Mahajjata kan Aikin Hajjin Shekarar 2026

"A Kula": Saudiyya Ta Gargadi Mahajjata kan Aikin Hajjin Shekarar 2026

  • Mahajjata daga kasashe daban-daban na duniya na ci gaba da gudanar da aikin hajjin shekarar 2026 a kasa mai tsarki watau Saudiyya
  • Hukumar kula da yanayi ta kasar Saudiyya ta bukaci mahajjata da su bi a hankali kam yanayin zafi, inda ta ba su shawarwarin matakan da ya kamata su dauka
  • An bukaci mahajjata da su rika yawo da laima domin kaucewa shan zafin rana yayin da suke zirga-zirga wajen gudanar da aikin hajji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Makkah, kasar Saudiyya - Hukumar kula da yanayi ta kasar Saudiyya ta gargaɗi mahajjata masu halartar aikin hajin shekarar 2026.

Hukumar ta gargadi mahajjata da su shirya wa matsanancin yanayin zafi, inda ake sa ran yanayin zafin zai tashi har zuwa digiri 47 na ma'aunin Celsius a lokacin gudanar da aikin hajjin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga: Matasa sun yi bore a Kano, sun kona wani ginin gwamnati

Saudiyya ta ja kunnen mahajjata
Mahajjata zaune cikin masallaci a Saudiyya Hoto: Haramain
Source: Facebook

Hukumomi a Saudiyya sun ja kunnen mahajjata

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto a ranar Laraba, 20 ga watan Mayun 2026 cewa hukumar ta buƙaci mahajjata da su ɗauki matakan kariya domin kauce wa rukunonin cututtuka da zafi ke haifarwa.

Hukumar ta bukaci su dauki matakan ne musamman a lokacin gudanar da ayyukan ibada na fili a Makkah da sauran wurare masu tsarki da ke kewaye, jaridar The Islamic Information ta kawo rahoton.

Bisa ga shawarwarin da aka bayar, an ƙarfafa gwiwar mahajjata da su riƙa ɗaukar laima yayin zirga-zirga tsakanin wurare daban-daban, kuma su riƙa shan ruwa akai-akai domin jikinsu kada ya bushe.

An ba mahajjata shawarar matakan dauka

Hukumomin sun kuma shawarci mahajjata da su guji daɗewa a ƙarƙashin hasken rana kai-tsaye a lokutan da zafi ya fi tsananta da rana, kuma su bi umarnin kiwon lafiya da tsaro da jami'an Saudiyya suka bayar a duk tsawon lokacin aikin hajjin.

Kara karanta wannan

Babban jami'i a gwamnatin Bauchi ya rasu a Makkah ana shirin fara aikin hajji

An kuma yaɗa lambar neman taimakon gaggawa ta Saudiyya, 997, domin mahajjata da ke buƙatar taimakon likita na gaggawa su yi amfani da ita.

Wannan gargaɗi yana zuwa ne yayin da miliyoyin mahajjata daga faɗin duniya ke ci gaba da isa Masarautar Saudiyya domin gudanar da aikin hajjin na shekara-shekara.

Saudiyya ta ja kunnen mahajjata kan yanayin zafi
Wasu mahajjata zaune a masallaci a Saudiyya Hoto: Haramain
Source: Facebook

Karanta wasu labaran kan aikin hajji

Mahajjatan Najeriya sun rasu a Saudiyya

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar kula ta Alhazai ta kasa (NAHCON), ta bayyana mahajjatan da ke fama da rashin lafiya da wadanda suka rasu a kasar Saudiyya.

Hukumar NAHCON ta bayyana cewa akalla mahajjatan Najeriya 54 ne ke kwance a asibitoci a kasar Saudiyya yayin gudanar da aikin Hajjin shekarar 2026.

Hakazalika, hukumar ta kuma tabbatar da rasuwar mahajjata guda hudu ‘yan Najeriya, wadanda dukkansu mata ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng