Za a Fara Aiki da Sabon Kudi a Najeriya da Kasashen ECOWAS a 2027

Za a Fara Aiki da Sabon Kudi a Najeriya da Kasashen ECOWAS a 2027

  • Ƙungiyar ECOWAS ta sake tabbatar da aniyarta na ƙaddamar da kuɗin bai ɗaya na yankin Yammacin Afirka mai suna ECO a shekarar 2027
  • Shugabannin ƙasashen ƙungiyar sun ce kuɗin zai ƙarfafa haɗin kan tattalin arziki da kasuwanci tsakanin ƙasashen yankin
  • ECOWAS ta kuma nuna damuwa kan matsalar tsaro a yankin Sahel da kuma yawaitar garkuwa da mutane musamman a Arewacin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Lungi, Saliyo – Ƙungiyar Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta sake jaddada kudirinta na ƙaddamar da kuɗin bai ɗaya na yankin mai suna ECO a shekarar 2027.

Shugabannin ƙasashen ƙungiyar sun bayyana hakan ne bayan kammala taron shugabannin ƙasashe karo na 69 da aka gudanar a birnin Lungi na ƙasar Saliyo ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasar, Julius Maada Bio.

Kara karanta wannan

Sojoji sun yi babban kamu a Borno, sun cafke ɗan kasar waje dake tallafawa ISWAP

Taron ECOWAS Sierra Leone
Lokacin da aka yi taron ECOWAS na 2026 a Sierra Leone. Hoto: ECOWAS
Source: Facebook

Leadership ta rahoto cewa shugabannin sun bayyana kuɗin ECO a matsayin wani muhimmin mataki na ƙarfafa haɗin kan tattalin arziki, bunƙasa kasuwanci da samar da ci gaba mai ɗorewa a faɗin yankin.

Batun kawo kudin ECO

A cikin sanarwar bayan taron, shugabannin ECOWAS sun ce duk da ƙalubalen tattalin arzikin duniya, tattalin arzikin ƙasashen yankin ya ci gaba da nuna juriya.

Sun bayyana cewa ana sa ran shekarar 2026 ta zo da kyakkyawan fata sakamakon raguwar hauhawar farashin kayayyaki, raguwar bashin gwamnati idan aka kwatanta da ƙarfin tattalin arziki da kuma ingantuwar kasuwanci da ƙasashen waje.

Sai dai sun yi gargaɗin cewa gibin kasafin kuɗin wasu ƙasashe na ci gaba da zama abin damuwa.

Vanguard ta wallafa cewa shugabannin sun ce:

"Hukumar ta sake tabbatar da cikakken aniyarta na ƙaddamar da kuɗin ECO a shekarar 2027 a matsayin muhimmin mataki na zurfafa haɗin kan tattalin arzikin yankin da kuma samar da ci gaba mai ɗorewa."

Kara karanta wannan

An yi girgizar kasa sau 2 a jere a Iran, wasu mutane sun jikkata

Yadda za a fara amfani da ECO

Bugu da kari, kungiyar ECOWAS ta bayyana cewa ba dukkan ƙasashe za su fara amfani da kuɗin ECO lokaci guda ba.

A cewarta, ƙasashen da suka cika sharuddan tattalin arzikin da aka gindaya ne za su fara amfani da kuɗin, yayin da sauran za su ci gaba da samun tallafi har sai sun cancanta.

Ƙungiyar ta kuma yi maraba da rajistar sunan "ECO" a Hukumar Kare Haƙƙin Mallakar Fasaha ta Afirka (OAPI), tare da umurtar hukumar ECOWAS da ta ci gaba da aiki don tabbatar da hakan.

Taron ECOWAS a Sierra Leone
Shugabanni a wajen taron ECOWAS a Sierra Leone. Hoto: ECOWAS
Source: Facebook

Ana amfani da N100 a Najeriya

A wani labarin, mun ruwaito cewa Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bayyana cewa takardar kuɗin N100 na ci gaba da kasancewa halastacciyar kuɗin ciniki a faɗin ƙasar.

Bankin ya umarci jama'a, 'yan kasuwa da bankuna da su daina ƙin karɓar takardar, yana mai cewa jita-jitar cewa an daina amfani da ita ba ta da tushe.

CBN ya ce takardar N100 na nan daram a matsayin kuɗin da doka ta tanada a Najeriya, kuma duk wanda ya ƙi karɓarta ya saɓa da ƙa'idodin kuɗin ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng