Kwalara na Kisa a Awanni, Gwamnatin Kano ta yi Gargadin Amfani da Ruwan Sama

Kwalara na Kisa a Awanni, Gwamnatin Kano ta yi Gargadin Amfani da Ruwan Sama

  • Yayin da aka samu barkewar amai da gudawa da aka fi sani da kwalera a Najeriya, gwamnatin Kano ta gargadi mazauna jihar kan matakan kare kansu da ma annobar a jihar
  • Wannan na zuwa ne yayin da damunar bana ta fara sauka, inda ma'aikatar lafiya ta jihar ta ce a rika kula sosai wajen sha da amfani da ruwan sama musamman na farko-farko
  • Kwamishinan lafiya na jihar, Dr. Abubakar Labaran Yusuf ya bayyana cewa ruwan saman farko-farko ba shi da kyau domin ya taro datti, kuma shan sa na tattare da hadari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kano- Gwamnatin jihar Kano ta gargadi mazauna jihar su yi ta'ammali da ruwan sama bayan an tsaftace shi saboda gudun bullar annobar amai da gudawa.

Kara karanta wannan

Sojoji sun tarwatsa 'yan ta'adda suna shirin taron kitsa manakisa a Kaduna, an kashe miyagu

A yanzu haka Najeriya na daga cikin kasashen duniya 24 da aka samu cutar, inda akalla mutane 40 suka riga mu gidan gaskiya, musamman a Kudancin kasar.

Abba k
Gwamnatin Kano ta bayar da shawara kan kare kamuwa da amai da gudawa Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Twitter

A sakon da shugaban sashen hulda da jama'a da ma'aikatar lafiya, Ibrahim Abdullahi ya wallafa a shafinsa na Facebook, gwamnatin ta gargadi jama'a da cewa idan ba dole ba, kada su yi amfani da ruwan sama.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Za mu sa ido kan lafiyarku," Dr. Yusuf

Yayin da ake cutar amai da gudawa ta barke a Najeriya har ta yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane 40, gwamnatin Kano ta ce ta na sanya ido kan lafiyar jama'ar jihar, kamar yadda Punch ta wallafa.

“Yana da kyau mutane su fahimci cewa, ruwan saman da ake yi a farkon damina ba mai kyau ba ne. Idan ya zama dole sai an yi amfani da shi, to a tabbata an yi amfani da dukkan sinadaran tsaftace ruwa; a dafa a tace kafin a yi amfani da shi. Yin haka zai taimaka sosai wajen hana kamuwa da cutar amai da gudawa".

Kara karanta wannan

Tsananin zafi ya yi sanadiyyar rayuka 900, musulmai na cigiyar 'yan uwansu

- Dr. Abubakar Labaran Yusuf

"Kwalera na kisa cikin awanni 2," Likita

Kwararren likitan iyali a asibitin Malam Aminu Kano, Dr. Shafi'i Umar ya ce mutum zai iya mutuwa a kasa da awanni biyu bayan fara amai da gudawa.

Dr. Shafi'i ya shaidawa Legit Hausa cewa da zarar mutum ya fara rasa ruwan jikinsa, zai iya mutuwa kafin a garzaya asibiti, musamman idan aka tsaya wasa.

Ya ce za a iya baya mutum agajin gaggawa na farko hadin ruwan gishiri da suga, ko a hada da karamin cokali daya na gishiri, cokali shida na suga kafin a je asibiti.

Kwalara ta bulla a Legas

A wani labarin kun ji gwamnatin Legas ta tabbatar da bullar annobar amai da gudawa a wasu daga kananan hukumomin jihar, ta kashe wasu da dama.

Kananan hukumomin da cutar ta fi kamari sun hada da Lagos Island, Kosofo da Eti yayin da yanzu haka ta kwantar da mutane akalla 400.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.