Amnesty Ta Zargi Gwamnatin Najeriya da Gazawa Wajen Kare Rayukan Jama'a
- Amnesty ta bayyana kokenta kan yadda gwamnatin Najeriya ke yiwa lamarin tsaro rikon ‘yan koyo a shekarun nan
- An sace mutane da dama tare da hallaka wasu mutane da dama a jihohin arewacin Najeriya, musamman Arewa maso yamma
- A halin yanzu, ana ci gaba da samun hare-hare a yankuna da dama, inda aka kashe daruruwan mutanen da basu ji ba basu gani ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Arewacin Najeriya - Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Amnesty International ta caccaki gwamnatin Najeriya, tana zarginta da rashin ɗaukar matakan da suka dace don kare rayuka da dukiyoyin 'yan ƙasa.
Wannan zargi ya fito ne bayan da rahotanni suka bayyana cewa wasu ‘yan bindiga sun hallaka fiye da mutum 20 a wani ƙauyen da ake hakar ma’adinai da ke jihar Zamfara, arewacin Najeriya.
Cikin wata sanarwa da Daraktan Amnesty International a Najeriya, Mallam Isa Sanusi, ya fitar, ya bayyana cewa aƙalla mutane 54 ne suka rasa rayukansu a hare-hare daban-daban da suka auku a arewacin ƙasar cikin ƴan kwanakin nan.

Asali: Facebook
Yadda lamarin ya auku
Isa Sanusi ya bayyana wa BBC cewa mutum 26 aka binne a ƙauyen Gobirawan Chali, inda ‘yan bindiga suka kai hari kan masu aikin hakar ma’adinai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa:
"Hare-haren baya-bayan nan sun sake bayyana cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ba ta da tsari mai ƙarfi na kawo ƙarshen ta’addancin da ya dabaibaye yankunan ƙasar. Yayin da mutane ke kara fuskantar hari, gwamnati tana kasa tsare rayukansu."
Wasu karin hare-haren
A cikin makon da ya gabata ne wasu ‘yan bindiga dauke da babura suka farmaki ƙauyen Gobirawan Chali da ke karamar hukumar Maru a jihar Zamfara, inda suka bude wa mazauna wuta kafin su fara shiga gidaje suna kashe mutane.
Rahotanni daga kafofin yaɗa labarai sun nuna cewa maharan sun kai farmaki wasu ƙauyuka biyu da ke makwabtaka da Gobirawan Chali.
Sai dai rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta ki bayyana wani abu dangane da hare-haren da aka kai a yankin duk da tambayoyin da aka yi mata.
Hari ya tsananta a Arewa
A makonnin da suka gabata ne kuma hare-hare suka tsananta a wasu jihohi kamar su Benue da Plateau, inda aka kashe mutane tare da kone gidaje da gonaki.
Haka nan a jihohin Sokoto da Zamfara, rahotanni sun nuna cewa ‘yan bindiga na ci gaba da kakabawa mazauna garuruwa haraji da wasu dokoki da karfi da yaji.
Amnesty International ta ce:
"Ganin yadda lamarin tsaro ke tabarbarewa a Najeriya, yana kara bayyana cewa kare rayukan jama'a da dukiyoyinsu ba ya daga cikin abubuwan da gwamnati ke mayar da hankali a kai."
Gwamnati ta gaza katabus kan lamarin tsaro
Ta kuma ƙara da cewa:
"Bai kamata a bar mutane cikin fargaba da tsoron fuskantar hari ko sacewa ba. An bar su cikin hannun ‘yan bindiga."
Rahotanni sun nuna cewa dubban mutane ne aka kashe, wasu kuma aka sace a yankin arewa maso yammacin Najeriya cikin shekaru biyu da suka gabata, sakamakon ƙarin tabarbarewar tsaro.
Sai dai a lokuta da dama, gwamnatin tarayya ta sha nanata cewa tana yin bakin ƙoƙarinta wajen magance matsalar tsaro a ƙasar.
Asali: Legit.ng