Sakon Uwargidan Tinubu ga Al’ummar Musulmi yayin da Ake Shirin Babbar Salla
- Uwargidan shugaban kasa, Oluremi Tinubu, ta shawarci ‘yan Najeriya su rungumi zaman lafiya da hadin kai yayin bikin sallah
- Sanata Oluremi Tinubu ta kuma roki jama’a su tallafa wa marasa galihu da masu bukata domin yada kauna, tausayi da sabunta fata a kasa
- Uwargidan shugaban kasar ta ce bikin salla lokaci ne na tunawa da sadaukarwa, biyayya ga Allah da addu’o’in samun zaman lafiya da ci gaba a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Uwargidan shugaban kasa, Oluremi Tinubu, ta bukaci ‘yan Najeriya su rungumi zaman lafiya tare da rayuwa cikin fahimtar juna a fadin kasa.
A sakonta na bikin babbar salla ga Musulmai a Najeriya da ketare, ta ce karfin Najeriya yana cikin hadin kai da mutunta juna tsakanin jama’a.

Source: Facebook
Babbar salla: Sahawar da Oluremi ta ba Musulmi

Kara karanta wannan
Dalilin da ya sa Tinubu ya cancanci 'yan Najeriya su kara ba shi dama a zaben 2027
Ta bayyana cewa wajibi ne ‘yan Najeriya su ci gaba da karfafa alakarsu tare da aiki tare domin gina kasa mai zaman lafiya da ci gaba, cewar rahoton The Nation.
Sanata Tinubu ta kuma bukaci jama’a su taimaka wa marasa galihu da masu bukata domin kawo sauki da sabunta fata ga rayuwarsu.
“Kada mu manta da hakikanin ma’anar wannan rana ta hanyar tallafa wa makwabtanmu, musamman marasa karfi da marasa galihu a cikinmu. Wadannan ayyukan alheri da karamci na iya sabunta fata tare da kawo sauki ga mutane da dama.”
A cewarta, ayyukan alheri da tausayi ga makwabta musamman masu rauni na daga cikin muhimman darussan da babbar salla ke koyarwa.

Source: Facebook
Muhimmancin babbar salla ga Musulmi
Uwargidan shugaban kasar ta ce bikin babbar salla lokaci ne na tunawa da sadaukarwa, biyayya, imani da nuna kauna ga al’umma baki daya.
Ta bayyana cewa ma’anar bikin ta wuce shagulgula kawai domin yana koyar da sadaukar da kai da mika wuya ga nufin Allah, cewar Punch.
Oluremi ya ce:
“Yayin da muke bikin, ina karfafa wa dukkan ‘yan Najeriya gwiwa su rungumi zaman lafiya tare da rayuwa cikin jituwa da fahimtar juna. Karfinmu a matsayin kasa yana cikin hadin kanmu, mutunta juna da kuma kudurinmu na gina al’umma mai cike da kauna da fahimtar juna.”
Ta kuma bukaci ‘yan Najeriya su ci gaba da yi wa kasa addu’ar samun dorewar zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaba mai anfani.
A karshe, ta yi wa Musulmai a Najeriya da sauran sassan duniya fatan gudanar da bikin babbar salla cikin farin ciki da kwanciyar hankali.
'Kalubalen tikitin Musulmi da Musulmi' - Oluremi
Mun ba ku labarin cewa uwargidan Shugaban Kasa, Oluremi Tinubu ta bayyana halin da ta shiga a lokacin da mai gidanta, Bola Tinubu ke neman kujerar mulkin Najeriya.
A cikin wani littafi da ta rubutu, ta bayyana cewa zaɓin takarar shugaban ƙasa da Tinubu ya yi a kan tikitin “Muslim‑Muslim” ya raba kan cocinta.
Oluremi Tinubu ta ce bakin jinin da wannan lamari ya jawo bai hana ta ci gaba da bauta wa Ubangijinta ba, har aka samu nasara.
Asali: Legit.ng
