Sarki Aminu Ado Bayero Ya Shirya Hawan Sallah a Kano, Ya Aika Saƙo ga Jami'an Tsaro
- Mai martaba Aminu Ado Bayero ya fara shirye-shiryen hawan sallah yayin da ake sa ran gudanar da idin babbar Sallah a 27 ga Mayu 2026
- Masarautar Kano ta ce an fara shirye-shiryen gudanar da bukukuwan daga ranar 27 ga Mayu kuma Alhaji Aminu Bayero zai yi hawa a dawakai
- Fadar Sarkin Kano na 15 ta bukaci hadin kan jami’an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya yayin gudanar da wadannan bukukuwan sallar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Kano - Sarkin Kano na 15, Aminu Bayero, ya sanar da jami’an tsaro a jihar Kano shirinsa na gudanar da bikin hawan babbar Sallah na shekarar 2026 daga fadar Nasarawa.
Rahotanni sun bayyana cewa masarautar ta aika wasiku daban-daban ga kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Ibrahim Bakori, da kuma Daraktan DSS na jihar domin sanar da su shirye-shiryen bikin.

Source: Facebook
Aminu Ado Bayero ya fara shirye-shiryen hawan Sallah
Wasikun dai an rubuta su ne ranar 17 ga Mayu, 2026, kuma sakataren Sarkin Kano mai zaman kansa, Abdullahi Kwaru, ne ya sanya hannu a kansu, in ji rahoton The Punch.
A cikin wasikun, masarautar ta bayyana cewa an riga an fara shirye-shiryen gudanar da bukukuwan Sallah da za su fara daga ranar 27 ga Mayu, 2026.
Masarautar ta ce shawarar gudanar da hawan Sallah ta biyo bayan tarukan da mambobin majalisar masarautar Kano suka gudanar.
Wasikar ta ce:
“Sakamakon tarukan da mambobin majalisar masarautar Kano suka yi ya nuna cewa za a gudanar da hawan Sallah kamar yadda tsarin masarauta ya tanada."
Masarautar Aminu Ado ta fadi muhimmancin hawan Sallah
Masarautar ta bayyana cewa Hawan Sallah na daga cikin manyan al’adun gargajiyar Kano da ake gudanarwa duk shekara.
Ta ce yayin bikin, 'Sarkin Kano' tare da hakimai da sauran masu fada a ji kan zagaya cikin birni a kan dawakai domin gaisawa da jama’a da kuma karbar mubaya’a daga al’umma, in ji rahoton Leadership Hausa.

Kara karanta wannan
2027: Kakakin majalisar Kwara ya raba gardama a zaben fitar da dan takarar gwamnan APC
Wasikun sun bayyana cewa:
“Bukukuwan hawan Sallah na daga cikin al’adun shekara-shekara da ke bai wa Mai Martaba damar zagaya gari tare da fadawansa a kan dawakai domin ganawa da jama’arsa."
Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da shari’ar da ta shafi sarautar Kano bayan gwamnatin jihar Kano ta tube Aminu Bayero tare da mayar da Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano na 16.

Source: Original
Aminu Ado Bayero ya nemi hadin kan jami’an tsaro
Duk da rikicin da ke gaban kotu, Aminu Bayero na ci gaba da gudanar da wasu harkokin masarauta daga fadar Nasarawa.
Masarautar ta tabbatar wa jami’an tsaro cewa za a gudanar da bukukuwan cikin lumana tare da neman goyon baya da hadin kansu.
“Muna fatan samun hadin kai da goyon bayan ku kamar yadda aka saba, kuma muna mika gaisuwar Mai Martaba gare ku,” in ji wasikun.
Sakon Aminu Bayero ga gwamnati a karamar Sallah
A wani labari, mun ruwaito cewa, Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya gudanar da sallar Idi a birnin Kano a ranar Juma'a, 20 ga watan Maris 2026.
Aminu Ado Bayero ya aika da sako ga gwamnatin tarayya da ta jihar Kano kan su ci gaba da kokari wajen sauke nauyin da ke kansu.
Mai martaba sarkin ya aika da sako na musamman ga Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf bayan kammala azumin watan Ramadan.
Asali: Legit.ng

