Hanyar Samun Tsira da Abubuwan da Limamin Arafa Ya Bayyanawa Musulmai

Hanyar Samun Tsira da Abubuwan da Limamin Arafa Ya Bayyanawa Musulmai

  • An yi hudubar Arafah a Masallacin Namirah a ranar 9 ga Zul-Hijjah, inda aka jaddada muhimmancin imani da tsoron Allah
  • Hudubar ta bayyana cewa Musulunci ginshiki ne na zaman lafiya da ceto a duniya da lahira, kuma ya ƙunshi matakai uku
  • Limamin ya yabawa shugabancin Saudiyya bisa jajircewarsu wajen sauƙaƙa aikin hajji da kuma tabbatar da tsari a wuraren ibada

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Saudiyya - Sheikh Saleh bin Abdullah Al Humaid ya gabatar da hudubar Arafah a Masallacin Namirah da ke cikin filin Arafah a ƙasar Saudiyya.

Sheikh Al Humaid ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su yi riƙo da gaskiya, imani da kyawawan ɗabi’u a rayuwarsu.

Saleh bin Abdullah Al Humaid ya jagoranci hudubar Arafa
Limamin Arafa ya fadi hanyar tsira a duniya da lahira. Hoto: Inside the Haramain
Asali: Facebook

Legit ta tattaro muhimman abubuwan da limamin ya mayar da hankali a kansu ne a cikin wani sako da shafin Inside the Haramain ya wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hudubar da ta fi mayar da hankali kan imani da tsoron Allah, ta bayyana cewa ana samun tsira duniya da lahira ne saboda bin dokokin Allah da rayuwa daidai da koyarwar Annabi (SAW).

Limamin ya karanta ayoyin Alƙur’ani da ke bayyana yadda Allah ke yin albarka ga masu tsoronsa, tare da basu lada mai yawa a rayuwar duniya da kuma lahira.

Arafa: Musulunci ne tushen zaman lafiya

Sheikh Abdullah Al Humaid ya bayyana cewa Musulunci shi ne addinin da Allah ya zaɓa wa bayinsa, kuma ya cika ni’imarsa ta hanyar saukar da shi.

Hudubar ta ce tsayawa kan addinin Allah da bin hanyarsa yana kawo kwanciyar hankali da nutsuwa a zukata da zaman lafiya rayuwar yau da kullum.

Malamin ya jaddada kira ga musulmi da su rungumi addini ta hanyar neman ilimi domin yin ibada yadda ya kamata.

Limamin Arafa ya ce imani na karuwa

Sheikh Al Humaid bayyana cewa imani yana da matakai da rassa da yawa, inda ya haɗa da magana, niyya a zuciya, da kuma aiki da gabobi.

Limamin ya kara da cewa imani yana karuwa inda ya ce yana ƙaruwa ne da biyayya, kuma yana raguwa saboda sabo.

Malamin ya ce daga cikin alamomin imani akwai: girmama iyaye, riƙon amana, faɗin gaskiya, daina magana marar amfani, da taimakon marayu da maƙwabta.

Ya bayyana cewa Manzon Allah (SAW) ya ce:

“Cikakken mumini shi ne mafi kyawun dabi'u.”

Limamin Arafa ya yabi Saudi kan aikin Hajji

Hudubar Arafa ta yaba da irin rawar da Saudiyya ke takawa a kowace shekara wajen shirya hajji da tabbatar da tsaro da walwala ga alhazai daga sassa daban-daban na duniya.

Ya yi kira ga mahajjata da su bi ƙa’idoji, su nuna haɗin kai da juriya don tabbatar da sahihancin aiwatar da ibada ba tare da rikice-rikice ko cikas ba.

Kiran mahajjata su yi addu'a a Arafa

A ƙarshe, limamin ya yi kira ga kowane mahajjaci da ya tuba ga Allah da zuciya ɗaya, ya kuma riƙa yin addu’a wa kansa da sauran bayin Allah.

Mahajjata na hawan Arafa a Saudiyya
An bukaci mahajjata su yi addu'a a ranar Arafa. Hoto: Getty Images
Asali: Facebook

Ya kuma jaddada cewa wannan rana ce mai tsarki da alfarmarta ta ke da girma a wajen Allah, don haka musulmi su amfana da ita wajen neman gafara da tsarkake zukata.

Sultan ya yi kira kan ranar Arafa

A wani rahoton, kun ji cewa mai alfarma sarkin Musulmi ya bukaci 'yan Najeriya su mayar da hankali kan ibada a ranar Arafa.

Sarkin ya ce addu'a na da muhimmanci a ranar Arafa, saboda haka ya bukaci Musulmai su dage da yinta a ranar.

Ya bayyana cewa yana da muhimmanci Musulmai su yi addu'a game da matsalolin tsaro da suka addabi Najeriya a ranar Arafa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng