‘Babu Afuwa’: Babban Limami Ya Fadi Abin da Kur’ani Ya Ce kan Yan Ta’adda
- Babban Limami a Najeriya ya bukaci gwamnati ta hallaka masu garkuwa da mutane a Najeriya bayan sace dalibai da malamai
- Malamin ya nuna takaici kan kisan wani malamin lissafi da ’yan bindiga suka yi, yana mai cewa irin wannan ta’asa ba ta cancanci gafara ba
- Limamin ya soki shirin yafiya ga ’yan bindiga da masu garkuwa, yana kira ga gwamnati ta dauki mataki mai tsauri domin dakile rashin tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ogbomoso, Oyo - Babban Limamin Ogbomoso, Yunus Teliat Olushina Ayilara II, ya nuna damuwa game da afuwa ga yan ta'adda.
Limamin ya bukaci gwamnatin Najeriya ta kashe masu garkuwa da dalibai, malamai da shugaban makaranta a Oyo.

Source: Facebook
Malamin ya bayyana haka ne yayin hudubar Juma’a da ya gabatar da harshen Yarbanci a Ogbomoso da ke Oyo, cewar rahoton Zagazaola Makama.
Malami ya fadi hukuncin Kur'ani kan yan ta'adda
Ya ce duk wanda aka kama kuma bincike ya tabbatar da cewa yana da hannu wajen garkuwa ko kashe mutane bai kamata a yi masa afuwa ba.
A cewarsa, Kur’ani ya tanadi hukuncin kisa ga masu irin wadannan munanan laifuka bayan tabbatar da gaskiyar abin da suka aikata.
Limamin ya nuna matukar takaici kan kisan wani malamin lissafi da ’yan bindiga suka kashe bayan ya sadaukar da rayuwarsa wajen koyar da yara.
Ya ce akwai mutane da dama da suka kasa ci gaba da karatu saboda rashin kwarewa a fannin lissafi duk da muhimmancin ilimin, kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito.
Ya ce:
“Idan gwamnati ta kama masu garkuwa da mutane, sannan bincike ya tabbatar cewa su ne suka sace dalibai, yara, malamai da shugaban makaranta, abin da Kur’ani mai tsarki ya ce shi ne kada a yafe musu, sai dai a kashe su nan take.”

Source: Original
Limami ya yi takaicin kashe malami
Ayilara ya bayyana cewa marigayin ya zabi hidimtawa al’ummarsa maimakon neman manyan ayyuka masu albashi a manyan kamfanoni.
Ya ce kashe irin wannan mutum mai amfani ga al’umma babban zalunci ne wanda bai kamata gwamnati ta yi wa masu laifin afuwa ba.
Malamin ya soki manufofin yafiya ga ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane, yana tambayar yadda za a gafarta wa masu aikata irin wannan ta’asa.
Ya ce duk wanda yake da zuciyar aikata kisan kai da garkuwa da mutane ba zai samu gafarar Ubangiji ba idan aka tabbatar da laifinsa.
Kalaman limamin na zuwa ne yayin da ake ci gaba da nuna damuwa kan yawaitar hare-haren ’yan bindiga da sace mutane a sassan Najeriya.
Ta'addanci: Lauya ya bukaci a kama Sheikh Gumi
Mun ba ku labarin cewa wani lauya mai rajin kare hakkin bil’adama ya bukaci gwamnatin tarayya ta kama Sheikh Ahmad Abubakar Gumi kan kalaman da ya yi kan matsalar tsaro.
Mai fafautukar kare hakkin bil Adama ya ce duk wanda ke nuna goyon baya ko tausaya wa ‘yan ta’adda ya kamata a dauke shi tamkar dan ta’adda.
Sheikh Gumi ya bayyana a wani bidiyo cewa Fulani makiyaya wani bangare ne na al’umma, yana mai cewa dole Najeriya ta koyi zama tare da su.
Asali: Legit.ng

