Gwamnatin Katsina Ta Yi Maganar 'Hadimin Gwamna' da Ake Zargi da Hannu a Garkuwa da Mutane

Gwamnatin Katsina Ta Yi Maganar 'Hadimin Gwamna' da Ake Zargi da Hannu a Garkuwa da Mutane

  • Gwamnatin Katsina ta ce ta jima da sallamar Nura Aliyu Garwa daga mukaminsa na mai taimaka wa gwamna kan harkokin ci gaban al’umma
  • Ana zargin tsohon hadimin gwamnan da alaka da wata kungiyar masu garkuwa da mutane da ake zargin ta sace yaro dan shekara takwas
  • Gwamna Dikko Radda ya nuna takaicinsa kan yadda tsohon hadiminsa ya shiga irin wadannan zarge-zarge, ya kuma yabi yan sanda

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Katsina, Nigeria - Gwamnatin jihar Katsina ta yi karin haske kan zargin da ake yi wa Nura Aliyu Garwa, Babban Mataimaki na Musamman (SSA) ga Gwamna Dikko Radda kan harkokin ci gaban al’umma.

Ana zargin hadimin gwamnan na cikin jagororin wata ƙungiyar masu garkuwa da mutane da ake alaƙanta ta da satar wani yaro ɗan shekara takwas a cikin birnin Katsina.

Kara karanta wannan

Bikin sallah: Gwamna Zulum ya raba shinkafa mai dauke da hoton Tinubu

Dikko Radda.
Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Radda yana magana da kwamishinoni a taron Majalisar zartarwa Hoto: Dr. Dikko Umaru Radda
Source: Facebook

Dikko Radda ya jima da sallamar Nura Garwa

Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnatin Katsina ta bayyana cewa Gwamna Dikko Radda ya jima da dakatar da Nura Garwa daga mukaminsa bisa wannan zargi da ake masa na hannu a garkuwa da karamin yaro.

Hakan na kunshe ne a a wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu na jihar, Bala Salisu Zango, ya fitar ranar Litinin, 25 ga watan Mayu, 2026.

Gwamnatin ta ce an dakatar da Garwa ne bisa zargin karkatar da kayan tallafi da aka ware domin raba wa mutanen Ƙaramar Hukumar Batsari ƙarƙashin shirin ci gaban al’umma na jihar Katsina

Sanarwar ta ƙara da cewa Garwa daga baya ya nuna sha’awar tsayawa takarar kujerar majalisar dokokin Jihar Katsina domin wakiltar Ƙaramar Hukumar Batsari.

Gwamna Dikko Radda ya yi takaicin lamarin

Sai dai gwamnatin ta bayyana cewa Gwamna Radda ya nuna takaici da damuwa kan zargin da ake yi masa, yana mai cewa abin takaici ne yadda mutum mai matsayi a gwamnati da burin siyasa zai iya shiga irin waɗannan zarge-zarge.

Kara karanta wannan

Albarkacin bikin babbar Sallah, gwamna zai fara rabon kayan abinci ga ma'aikata

Haka kuma, gwamnan ya yaba wa rundunar yan sandan Katsina da sauran hukumomin tsaro bisa ƙoƙarinsu wajen yaƙi da rashin tsaro da ci gaba da gudanar da ayyukan daƙile laifuffuka.

Dalilin fara zargin tsohon hadimin gwamnan

A baya-bayan nan ne rundunar ‘yan sandan Katsina ta bayyana wasu mutane da ake zargi da hannu a ayyukan wata ƙungiyar masu garkuwa da mutane.

Ana zargin kungiyar da satar wani yaro ɗan shekara takwas a unguwar Sardauna Estate da ke cikin birnin Katsina, inda aka ce tsohon hadimin gwamnan na daga cikin waɗanda ake zargi.

Katsina.
Taswirar jihar Katsina da ke Arewa maso Yammacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jaridar Punch ta ce lamarin ya jawo damuwa matuƙa a tsakanin al’umma sakamakon yadda ake zargin wani tsohon jami’in gwamnati da hannu a ayyukan ta’addanci da garkuwa da mutane.

Katsina ta goyi bayan kafa yan sandan jihohi

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya ce yana goyon bayan kafa rundunar ’yan sandan jihohi.

Gwamna Radda ya jaddada cewa yana da kyau a dauki dukkanin matakan da suka dace domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Ya jaddada bukatar kafa ’yan sandan jihohi domin bai wa jihohi damar tunkarar ƙalubalen da rashin tsaro ke haifarwa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262