Yan bindiga sun koma hanyar Kaduna-Abuja, sun yi awon gaba da mutane: Shehu Sani, Matafiya

Yan bindiga sun koma hanyar Kaduna-Abuja, sun yi awon gaba da mutane: Shehu Sani, Matafiya

- Bayan watanni, masu garkuwa da mutane sun tare hanyar Kaduna-Abuja

- Tun lokacin da aka tura jami'an Soji mata rabon da a tare hanyar

- Wani mai idon shaida ya ce wannan abu ya bashi tsoro

Yan bindiga masu garkuwa da mutane sun koma hanyar Abuja-Kaduna yayinda suka tare matafiya a ranar Juma'a kuma sukayi awon gaba da wasu, tsohon Sanata Shehu Sani da wani matafiyi sun bayyana.

According to Shehu Sani who said he received a distress call from a traveller, ”the bandits blocked the road between Jere and Katari at about 4 pm”.

A cewar Shehu Sani, wani matafiyi ya kirasa a waya cewa yan bindiga sun tare hanyar tsakanin garin Jere da Katari misalin karfe 4 na rana.

"Na samu kira cewa yan bindiga sun tare da hanyar Kaduna-Abuja, tsakanin Jere da Katari da tsakar rana, " yace.

"An yi awon gaba da dimbin mutane yayinda wasu suka juya da motocinsu duk da harbin yan bindigan."

DUBA NAN: Nan da shekara 2, har yan adawa sai sun jinjinawa shugaba Buhari: Fadar Shugaban kasa

Yan bindiga sun koma hanyar Kaduna-Abuja, sun yi awon gaba da mutane: Shehu Sani, Matafiya
Yan bindiga sun koma hanyar Kaduna-Abuja, sun yi awon gaba da mutane: Shehu Sani, Matafiya Hoto: kdsg
Asali: UGC

DUBA NAN: Nan da watan Yuli zamu fara ginin layin dogon Kaduna zuwa Kano, Minista Amaechi

Wani matafiyi @jpjohnson61 ya tabbatar da labarin inda yace a idonsa abin ya faru.

"Ban taba tsoro a rayuwata irin wannan ba. Abubuwa sun yi sauki yanzu, Sojoji sun mamaye wajen. Saura kiris ta ritsa da mu," yace.

Wakili Legit ya tuntubi kakakin yan sandan jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, amma bai daga waya ba.

A bangare guda, akalla mutane 10 ne suka gamu da ajalinsu a hannun yan bindiga yayin hari da harin ramuwar gayya da suka kai a wasu kauyuka da ke karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna

A cewar kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwan, yan bindigan sun kai hari kauyen Na'ikko a karamar hukumar Giwa inda suka yi musayar wuta da wasu yan garin hakan ya yi sanadin mutuwar mutane uku yan garin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel