Ta Faru Ta Kare: Kotu Ta Yanke wa Kwamandojojin Ansaru Hukuncin Daurin Rai da Rai

Ta Faru Ta Kare: Kotu Ta Yanke wa Kwamandojojin Ansaru Hukuncin Daurin Rai da Rai

  • Kotun Tarayya ta yanke wa kwamandojin Ansaru hukuncin daurin rai da rai bayan sun amsa laifuffuka 32 da suka hada da ta'addanci da garkuwa da mutane
  • Wadanda aka yanke wa hukuncin su ne Abubakar Abba da Mahmud Usman wadanda jami'an tsaro suka kama a bara kuma suka amsa laifinsu a gaban kotun
  • Mai shari'a Emeka Nwite ya yanke musu hukuncin daurin rai da rai kan wasu tuhume-tuhume, tare da Karin shekaru 20 kan sauran tuhume-tuhumen da aka musu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida.

Abuja - Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja a ranar Litinin ta yanke wa wasu mutum biyu da ake zargin kwamandojin kungiyar Ansaru ne hukuncin daurin rai da rai, bayan sun amsa laifinsu na tuhume-tuhume 32 da suka shafi ta'addanci.

Kara karanta wannan

Mutane 9 da aka sace sun taki sa'a, sun shammaci 'yan bindiga a jihar Katsina

Wadanda aka yanke wa hukuncin su ne Abubakar Abba (wanda aka fi sani da Abu Bara’a) da kuma Mahmud Usman (wanda aka fi sani da Isah Adam da Mahmud).

Kotu ta yanke wa wasu kwamandojojin Ansaru biyu hukuncin daurin rai da rai
Kwamandojin Ansaru biyu, Abubakar Abba (Abu Bara'a) da Mahmud Usman (Isah Adam) da aka yanke wa hukuncin daurin rai da rai. Hoto: @Abdulfagge
Source: Twitter

Yadda shari'ar kwamandojin Ansaru ta kasance

Hukumar tsaro ta farin kaya (SSS) ce ta gurfanar da su a madadin gwamnatin tarayya, kamar yadda rahoton Premium Times ta ruwaito.

Alkalin kotun, Mai shari'a Emeka Nwite, ya yanke hukuncin ne bayan wadanda ake tuhumar, wadanda jami'an tsaron Najeriya suka kama a bara, suka sauya laifinsu daga "ba su da laifi" zuwa "sun amsa laifinsu" a ranar Litinin.

Alkalin ya yanke wa mutanen biyu hukuncin daurin rai da rai kan tuhuma ta 30 da 31. Kazalika, ya kuma yanke musu shekaru 20 a kowanne daya daga cikin sauran tuhume-tuhumen, inda ya bayar da umarnin cewa a fara kirga zaman gidan yarin ne tun daga ranar da aka kama su.

Tuhume-tuhumen da ake yi msu

A ranar 11 ga watan Satumbar 2025 ne SSS ta fara gurfanar da kwamandojin kungiyar ta Ansaru a gaban kotun kan tuhume-tuhume 32 da suka shafi ta'addanci.

Tuhume-tuhumen 32 din sun hada da ta'addanci, daukar nauyin ta'addanci, garkuwa da mutane don neman kudin fansa, hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba, kera bama-bamai da sauran laifukan da suka shafi hakan.

Kara karanta wannan

Kotun daukaka kara ta jikawa INEC aiki, ta soke wasu sassan dokar zabe ta 2026

Hukumar ta kuma zarge su da jagorantar wasu rukunin kungiyoyin asiri, shirya hare-hare, da kuma kula da alaka da kungiyoyin ta'addanci masu biyayya ga Al-Qaeda da ke gudanar da ayyukansu a yankunan Sahel da Maghreb.

Sauya jawabi a kotu

A baya dai wadanda ake tuhumar sun musanta laifukan. Daga baya shari'ar ta tsaya cak bayan lauyan wanda ake kara, Bala Dakum, ya koka da cewa jami'an SSS sun hana shi ganawa da wadanda ake kara don shirya kariya gare su.

A lokacin da aka ci gaba da sauraron karar, bangaren masu kara ya fara gabatar da shaida daga wani jami'in SSS da aka sakaya sunansa da "Triple A," in ji rahoton Punch.

Babbar kotun tarayya ta yanke hukuncin daurin rai da rai kan kwamandojin Ansaru da aka kama.
Babbar Kotun Tarayya da ke birnin Abuja inda aka yanke wa kwamandojin Ansaru hukuncin kisa. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Shaidar ya fadawa kotun cewa wadanda ake tuhumar sun amince cewa sun karbi horo kan amfani da makamai a kasar Libya, sun kuma tabbatar da kasancewarsu mambobin Ansaru tare da kula da alaka da kungiyoyin ta'addanci da ke aiki a yankin Sahel da Maghreb.

A ranar Litinin din ne wadanda ake tuhumar suka yanke shawarar sauya jawabin na farko, lamarin da ya sa kotun ta bayar da umarnin a sake karanta musu tuhume-tuhume 32 din tun farko.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: Ƴan sanda sun cafke mayakan Lakurawa da ke addabar garuruwan Arewa

Sun amsa laifinsu kan kowanne daya daga cikin tuhume-tuhume 32 din a yayin da jami'in kotu yake karanta su daya bayan daya ga mutanen biyu.

An cafke jagoran Ansaru a Najeriya

A wani labari, mun ruwaito cewa, Jami’an tsaron Najeriya sun kama shugaban kungiyar ta’addanci ta Ansaru da ake nema ruwa a jallo, Abu Baraa.

Ana zargin shugaban kungiyar ta Ansaru, Abu Baraa da aka kama ne da shirya manyan hare-hare da dama a kasar nan.

Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai na musamman da aka gudanar a cibiyar yaki da ta’addanci ta kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com