Babbar Salla: Gwamna Ya Gindaya Sharuda ga Masu Sayar da Raguna, Shanu a Titi
- Gwamnatin Oyo ta tura gargadi mai zafi ga mazauna jihar da masu sayar da dabbobi da suka hada da shanu da raguna
- Majiyoyi sun tabbatar da cewa an kafa doka domin tabbatar da samun tsaro yayin da ake shirin bukukuwan salla babba
- Mahukunta da masu ruwa da tsaki sun bayyana cewa dokar hana kiwo a bude ba ta da nufin tauye wata kabila
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ibadan, Oyo - Gwamnatin Oyo ta kakaba doka ga masu sana'ar sayar da dabbobi da suka hada da awaki, tumaki, raguna da shanu.
Gwamnatin ta gargadi mazauna jihar da masu sayar da dabbobi da su guji sayar da shanu da raguna a manyan tituna yayin babbar salla.

Source: Facebook
An cimma wannan matsaya ne a wani taron masu ruwa da tsaki kan bin dokar hana kiwo a bude da aka gudanar a Ibadan, babban birnin jihar, cewar Punch.
Oyo: An kafa doka ana shirin bikin salla
A cikin sanarwar bayan taron, gwamnatin ta bayyana cewa akwai kasuwannin da aka ware domin sayar da dabbobi a dukkan kananan hukumomin jihar.
Masu ruwa da tsakin sun amince da bukatar tabbatar da cikakken bin dokar, suna masu cewa hakan zai taimaka wajen inganta lafiya da bunkasa tattalin arziki.
Matakin ya biyo bayan shirye-shiryen gudanar da bikin babbar salla mai zuwa a fadin kananan hukumomi 33 na jihar.
Shugabar hukumar, Mai shari’a Aderonke Aderemi mai ritaya, ta ce bin doka shi ne ginshikin zaman lafiya, tsaro da ci gaban kowace al’umma.
Ta bayyana cewa an kafa dokar ne domin magance rikicin manoma da makiyaya, lalata gonaki, barazanar tsaro da kuma matsalolin rayuwar jama’a.

Source: Original
An shawarci al'umma kan bin doka
Aderemi ta kara da cewa doka ba za ta yi tasiri ba idan ba a mutunta ta tare da tabbatar da aiwatar da ita yadda ya kamata ba, cewar Daily Post.
Ta ce wajibi ne gwamnati, jami’an tsaro, shugabannin al’umma, manoma da makiyaya su hada kai domin tabbatar da zaman lafiya da bin doka.
Ta kuma gargadi cewa duk wanda aka kama yana sayar da raguna da shanu a manyan tituna ko wuraren da ba a amince da su ba, za a kwace dabbobin tare da ci tarar mai laifin.
Kwamishinan noma da raya karkara na jihar, Olasunkanmi Olaleye, ya roki mazauna jihar su mutunta dokar, yana mai cewa hakan ne mafita ga rikicin manoma da makiyaya.
UAE: An kayyade farashin dabbobin layya
A wani labarin, an ji cewa hukumomi a Haddadiyar Daular Larabawa sun amince da ƙayyadadden farashin dabbobin layya na shekarar 2026 da muke ciki.
Farashin dabbobin ya fara ne daga Dirham 350 zuwa Dirham 800, ya danganta da nau'in dabba da kuma inda za a gudanar da yanka da rarrabawa.
Ana sa ran yin sallar layya ta shekarar 2026 a ranar 27 ko 28 ga watan Mayu, abin ya danganta da ranar da aka ga jinjirin watan Zul Hijjah.
Asali: Legit.ng

