Yadda Aka Ci Zarafin Musulmi kan Radin Suna a Najeriya, Kungiya Ta Yi Korafi
- Kungiyar Musulmi ta ITOON ta kai korafi ga ‘yan sanda da DSS kan zargin cin zarafi da barazana ga Musulmai a yankin Kudu maso Yamma
- ITTOON ta nuna damuwa kan abin da ta kira cin zarafin Musulmi da kalaman kiyayya a kafafen sada zumunta
- Shugaban kungiyar Sheikh Uwais Olanrewaju ya gargadi cewa rashin daukar mataki kan cin zarafin addini na iya kara haddasa rarrabuwar kawuna a kasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ikeja, Lagos - Kungiyar 'Islamic Training Organisation of Nigeria', wato ITOON, ta yi korafi kan zargin cin zaraiin yara Musulmi a yankin Kudu maso Yamma.
Kungiyar ta kai koke ga kwamishinonin ‘yan sanda da DSS na Lagos da Ogun kan cin zarafin Musulmi.

Source: Original
Kungiyar karkashin jagorancin Sheikh Uwais Olanrewaju ta ce ta dauki matakin ne bayan suka daga yanar gizo kan jaruman Nollywood da ke bin addinin Musulunci, cewar Tribune.
Yadda aka ci zarafin Musulmi a Lagos, Ogun
Rahotanni sun ce wasu masu amfani da kafafen sada zumunta sun yi ba’a ga sunayen Musulunci da aka sanya wa jariran ‘yan ukun da aka haifa.
ITOON ta bayyana lamarin a matsayin abin takaici da rashin tausayi, tana cewa an ci zarafin kananan yara ne saboda asalinsu na addini.
Kungiyar ta nuna damuwa musamman kan kalaman wani mai suna MS Baba wanda ake zargi da kiran jariran bayi a kafafen sada zumunta.
Sheikh Olanrewaju ya ce ‘yancin fadin albarkacin baki bai kamata ya zama damar cin zarafi ko kai hare-haren addini ga mutane ba.
Ya jaddada cewa kundin tsarin mulkin Najeriya ya bai wa kowa damar gudanar da addininsa da tarbiyyar ‘ya’yansa ba tare da tsoratarwa ba.
Kungiyar ta gargadi cewa ci gaba da yin shiru kan nuna kyamar addini a yanar gizo na iya kara haddasa rarrabuwar kawuna a kasa, cewar Daily Post.

Source: Twitter
Yadda aka samu rarrabuwar kai tsakanin Musulmi, Kirista
Yankin Kudu maso Yamma na kunshe da Musulmai da Kirista wadanda suka shafe shekaru suna zaman lafiya duba da cewa ana iya samun addinai daban-daban a cikin iyali daya.
Sai dai kwadayin shugabanci da mulki yana daga cikin abin da ke kara rarraba kan al'umma a yankin yayin Musulmi ko Kirista ke cewa lokacin da za a ba su dama ya yi.
Misali a Oyo, wata kungiyar Musulmi mai suna MUSCOYS ta bukaci gwamnan jihar, Seyi Makinde ya tuna da su a zabe mai zuwa.
Kungiyar Musulmi ta bukaci ya nuna soyayya da adalci ta hanyar goyon bayan dan takarar Musulmi a karkashin jam’iyyar PDP a zaben gwamna mai zuwa.
Musulmi ya ba coci kyautar wurin ibadah
Mun ba ku labarin cewa wani Musulmi a jihar Oyo ya yi abin a yaba da ya ba cocin St John kyautar makeken dakin taro domin cigaba da ayyukansu.
Musulmin mai suna Ahmed Raji ya ce ya ba da kyautar saboda yadda cocin bai nuna wariya ga sauran addinai da ke yankin Iseyin a Oyo.
Alhaji Raji ya bayyana himmatuwarsa wurin tabbatar da ba da goyon baya da kuma gudunmawa ga cocin a kowane lokaci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

