Majalisar Amurka Ta Shirya Kawo wa Trump Cikas game da Yaki da Kasar Iran

Majalisar Amurka Ta Shirya Kawo wa Trump Cikas game da Yaki da Kasar Iran

  • Ƴan majalisar Amurka sun amince da fara tattauna kudirin da zai dakile shugaba Donald Trump kan karfin ikonsa game kai hare-hare
  • Kudirin zai tilasta Shugaba Trump dakatar da yakin Iran ko neman amincewar majalisa kafin aiwatar da wani abu a yaki
  • Sanata Bill Cassidy na jam’iyyar Republican ya hada kai da ‘yan Democrat bayan zargin gwamnatin Trump da boye bayanan aikin 'Operation Epic Fury' ga majalisa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, US - Majalisar Dattawan Amurka ta amince da fara duba kudirin da zai kawo karshen ikon Donald Trump a yaki.

Majalisar za ta yi duba kan kudirin domin tilasta Shugaba Trump kawo karshen yakin Iran wanda ake ci gaba da yi a yankin Gabas ta Tsakiya.

Majalisar Amurka za ta kawo kudirin hana Trump yakin Iran
Jagoran addini a Iran, Mojtaba Khamenei da Shugaba Donald Trump na Amurka. Hoto: Imam Mojtaba Khamenei, Donald J Trump.
Source: Facebook

Kudirin da majalisar Amurka ke shirin kawowa

Kara karanta wannan

Sanata zai rikita APC, ya yi watsi da sakamakon zaɓen fitar da gwani a Cross River

Rahoton The New York Times ya ce kudirin zai iya zama na tilasta Trump don neman izinin majalisa domin ci gaba da kai hare-hare.

‘Yan Democrat tare da wasu ‘yan Republican hudu ne suka mara wa kudirin baya domin tabbatar da hakan ya tabbata.

Sanata Bill Cassidy daga Louisiana ya sauya matsayarsa bayan ya sha kaye a zaben fitar da gwani na jam’iyyarsa.

Ya ce gwamnatin Trump ta boye bayanai kan aikin soja mai suna 'Operation Epic Fury' daga majalisa da sauran ‘yan kasa.

Kuri’ar ta kare da sakamako 50 kan 47 domin amincewa da tattauna kudirin cikin makwanni masu zuwa.

Sanata John Fetterman ne kadai daga Democrat da ya goyi bayan Republican wajen adawa da kudirin a majalisar.

Rahotanni sun nuna cewa wasu ‘yan Republican sun fara nuna shakku kan yadda Trump ke tafiyar da rikicin Iran.

Trump zai gane da cikas a yaƙi da Iran
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump yana jawabi a fadar White House da ke Washington D.C. Hoto: Drew Angerer.
Source: Getty Images

Yadda ƴan majalisa ke kin jinin yakin Iran

Hakan na da nasaba da tsagaita wuta da ake ganin mai rauni ce, kuma suna shirye su kalubalanci shugaban kasa.

Shugaban marasa rinjaye na Democrat a Majalisar Dattawa, Chuck Schumer kafin kada kuri’ar ya caccaki Trump inda ya kwatanta shi da ƙaramin yaro.

Kara karanta wannan

Abin da Trump ya ce game da shirin kai wa Iran sabon hari

Ya ce:

“Wannan shugaban kasa kamar karamin yaro ne da ke wasa da bindiga mai harsashi, idan akwai lokacin da ya kamata a goyi bayan kudirin ikon yaki domin janye sojoji daga rikicin Iran, to yanzu ne."

Hakan ya biyo bayan gazawar shugaba Trump wajen neman izinin majalisa bayan wa’adin kwanaki sittin da doka ta tanada.

Bill Cassidy ya bayyana cewa jama’a da dama a Louisiana har da magoya bayan Trump suna nuna damuwa kan yakin Iran.

Ya ce babu dalilin amincewa da karin wa’adin yakin har sai gwamnati ta bayyana gaskiya ga majalisa, cewar rahoton Al Jazeera.

Iran: Dalilin Trump na yarda da tsagaita wuta

A baya, mun ba ku labarin cewa shugaba Donald Trump na Amurka ya yi magana game da yarjejeniyar zaman lafiya da Iran a yakin da ake yi.

Trump ya ce Amurka ta amince da tsagaita wuta da Iran ne bayan roƙon wasu ƙasashe ba don ra’ayinta kai tsaye ba.

Shugaban Amurka ya yi ikirarin cewa sojojin ƙasarsa sun lalata rundunar Iran gaba ɗaya, yana mai cewa har yanzu suna iya “gyara lamura” a ƙasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.