Ku kare kanku idan an kawo muku hari, IGP ya fada wa 'Yan sanda
- Shugaban ƴan sandan Najeriya, Muhammad Adamu ya yi kira ga ƴan sanda a kasar su kare kansu idan an kai musu hari
- IGP Adamu ya yi wannan furucin ne cikin jawabin da ya yi a hedkwatar rundunar da ke Abuja bayan ziyarar ganin ido
- Shugaban ƴan sandan ya ce ɓata garin da suka shigar rigar zanga-zanga nufin su shine karya wa ƴan sanda kwarin gwiwa
Babban sifetan ƴan sandan Najeriya, IGP, Mohammed Adamu a ranar Juma'a ya faɗa wa jami'an rundunar su kare kansu idan aka kai musu hari a gari kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Shugaban ƴan sandan ya yi jawabi ne a hedkwatar rundunar da ke Abuja bayan ziyarar zagaye da ya yi don ƙarfafawa gwiwar jami'an da wasunsu sun dena fita tituna.
Adamu ya kuma ce masu zanga-zangar EndSARs sunyi yunkurin rage wa ƴan sandan ƙwarin gwiwa amma rundunar za ta fito da tsarin tallafawa wadanda suka rasa rayukansu.

Asali: Twitter
DUBA WANNAN: 'Farautar 'yan bindiga suke yi' - Gwamnatin Kaduna ta yi karin haske kan jiragen sojoji da ke shawagi a jihar
A baya-bayan nan ɓata gari da suka shiga rigar zanga-zangar EndSARs sun rika kaiwa ƴan sanda hari a sassan ƙasar.
Daily Trust ta ruwaito cewa ƴan sanda 22 ne fusatattun masu zanga-zangar suka kashe a sassan ƙasar.
KU KARANTA: Zulum ya bayyana matakin da zai dauka kan ɓata garin da aka yi haya don yin zanga zanga a Borno
An kuma ƙone ofishin ƴan sanda 205 tare da wasu kamfanoni da gine-ginen gwamnati da na ƴan kasuwa masu muhimmanci.
A wani labarin, 'yar majalisar mai wakiltar mazaɓar Amuwo Odofin ta 1 a Jihar Legas, Mojisola Alli-Macaulay ta ce mafi yawancin matasan Najeriya cikin mayen ƙwayoyi suke a kullum.
Alli-Macaulay ta bayyana hakan ne yayin zaman majalisar jihar Legas da aka yi kan sata da ɓarna da ɓata gari suka yi sakamakon zanga-zangar EndSARs a cewar rahoton The Punch.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng