Kwamishinan Yan sandan Lagos ya ɗauki ƙwaƙkwaran Mataki don gujema abinda ya faru a Owerri

Kwamishinan Yan sandan Lagos ya ɗauki ƙwaƙkwaran Mataki don gujema abinda ya faru a Owerri

- Kwamishinan yan sandan jihar Lagos ya fara ɗaukar matakai a gidajen gyaran hali dake jihar biyo bayan harin da aka kai Owerri, jihar Imo

- Kwamishinan ya turo da ƙarin jami'an yan sanda zuwa kowanne gidan gyaran hali dake faɗin jihar

- A kwanakin baya ne wasu yan bindiga suka kai hari gidan gyaran hali a Owerri, jihar Imo, inda suka buɗe kofa fursunoni suka tsere

Kwamishinan yan sandan jihar Legos, CP Hakeem Odumosu, ya tura ƙarin jami'an yan sanda zuwa gidan gyaran hali 'Prison' dake faɗin jihar.

An bayyana haka ne bayan kwamishinan ya karɓi baƙuncin shugaban jami'an dake kula da gidan gyaran hali na jihar Lagos, Francis Adebisi, tare da tawagarsa a hedkwatar yan sanda dake babban birnin jihar, Ikeja.

KARANTA ANAN: Shehu Sani ga tsohon IGP: Sai wata rana Adamu, ka huta sosai don ka ciko daga ramar da kayi

A ɗan taƙaitaccen bayanin taron da mai magana da yawun 'yan sandan jihar, Olumuyiwa Adejobi, yasa a shafinsa na tuwita ya ce:

"Yanzu haka Kwamishinan yan sandan jihar Lagos, CP Hakeem Odumosu, ya shiga tattaunawa da contolan jami'an kula da gidan gyaran hali, Comp Francis Adebisi, tare da tawagarsa."

"Shugabannin biyu, zasu tattauna kan yadda za'a yi ƙoƙarin kare hare-hare a gidan gyaran hali."

Harin Owerri: Kwamishinan Yan sandan Jihar Lagos ya ɗauki ƙwaƙkwaran Mataki don gujema abinda yafaru a Owerri
Harin Owerri: Kwamishinan Yan sandan Jihar Lagos ya ɗauki ƙwaƙkwaran Mataki don gujema abinda yafaru a Owerri Hoto: @LagosPoliceng
Source: Twitter

Kwamishinan yan sandan ya ce na tura ƙarin jami'an yan sanda zuwa gidajen gyaran hali dake faɗin jihar mu ta Lagos don ƙara tsaurara tsaro.

KARANTA ANAN: Gurgu ya hargitsa gangamin APC, ya yi wa Shugaban karamar hukuma ihun ‘Ba mu so’

Sai dai ana ganin wannan matakin da kwamishinan ya ɗauka, bazai rasa alaƙa da harin da wasu yan bindiga suka kai gidan gyaran hali a Owerri Jihar Imo ba.

Inda a harin da yan bindigan suka kai ranar Litinin, sun kuɓutar da fursunoni kimanin 1,884, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Hakanan, yan bindiga sun kaima hedkwatar yan sanda ta jihar Imo hari a rana ɗaya da wancan harin, inda suka ƙona motocin jami'an yan sandan dayawa.

A wani labarin kuma Kasar Indiya ta baiwa Najeriya gudunmuwar rigakafin Korona guda 100,000

Allurar rigakafin Covishield da ƙasar Indiya ta yi ma Najeriya alƙawarin kawo wa a matsayin gudummuwa ta iso Najeriya.

Shugaban kwamitin yaƙi da cutar korona, Boss Mustapha ne ya bayyana haka a taron da kwamitinsa ya saba yi duk sati.

Source: Legit

Online view pixel