Gowon Ya Fadi yadda Obasanjo Ya Bijire Masa kan Aiki ƙarƙashin Murtala a yaƙin Biyafara
- Janar Yakubu Gowon ya bayyana yadda Olusegun Obasanjo ya watsi da shawarar da ya ba shi lokacin yakin basasa a Najeriya
- Gowon ya ce Obasanjo ya ƙi yin aiki ƙarƙashin Murtala Muhammed a lokacin yaƙin saboda batun girman matsayi
- Ya ce ya tilasta wa Obasanjo ya amince da umarnin gwamnati, sannan ya yaba masa kan biyayya da kishin ƙasa a lokacin yaƙin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Janar Yakubu Gowon mai ritaya ya bayyana wasu abubuwa da suka faru lokacin yakin basasa da aka yi a Najeriya a shekarun baya.
Gowon ya ce tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo ya taɓa ƙin yin aiki ƙarƙashin marigayi Murtala Muhammed lokacin yaƙin basasar Najeriya.

Source: Getty Images
Gowon ya bayyana hakan ne a cikin littafinsa mai suna “My Life of Duty and Allegiance” wanda aka ƙaddamar a Abuja, cewar Punch.

Kara karanta wannan
Duk da ƙaryata Amurka, an tabbatar da hannun Trump a hallaka jagoran ISIS a Najeriya
Dalilin Obasanjo na kin karbar umarni daga Murtala
Ya ce Obasanjo ya shaida masa kai tsaye cewa ba zai taɓa karɓar umarni daga Murtala ba saboda yana ganin ya fi shi girman matsayi a soja.
Sai dai Gowon ya ce a matsayinsa na babban kwamandan ƙasa, ya dage kan cewa yana da ikon tura jami’ai duk inda gwamnati ke buƙatarsu.
A cewarsa, daga baya Obasanjo ya amince da aikin, inda ya jagoranci wata runduna a Ibadan domin kula da tsaro da kayan tallafi a yankin Yamma.
Gowon ya yaba wa Obasanjo saboda yadda ya gudanar da aikinsa cikin nasara tare da nuna biyayya da kishin ƙasa a lokacin yaƙin basasar Najeriya.
Ya ce Obasanjo ya hana yunƙurin marubuci Wole Soyinka na taimaka wa Kanal Victor Banjo shiga yankin Yamma ta hanyar Benin zuwa Ibadan.

Source: Twitter
Tarihin haduwar Yakubu Gowon da Obasanjo
Tsohon shugaban ƙasar ya kuma bayyana yadda ya fara haɗuwa da Obasanjo a Birtaniya a shekarar 1958 lokacin horon jami’an soja na Najeriya.
A cewarsa, Obasanjo ya taimaka masa da kuɗi lokacin da ya isa Landan ba tare da isasshen kuɗin biyan kuɗaɗensa ba a sansanin jami’ai.
Ya bayyana Obasanjo a matsayin jami’i mai nutsuwa da hankali, duk da cewa ya ce wasu ƙananan jami’ai sun fi shi saurin fahimta a lokacin, cewar Daily Post.
Gowon ya kuma bayyana Murtala Muhammed a matsayin zaɓinsa na farko wajen jagorantar rundunar 2 Division saboda jarumtaka da ƙwazon da yake nunawa.
Sai dai ya ce Murtala yana yawan bari zuciya da fushi su rinjayi tunaninsa, duk da irin ƙwazon da ya nuna a lokacin yaƙin basasa.
Gowon ya fadi dalilin yakin basasa
A baya, an ji cewa Janar Yakubu Gowon ya ce yarjejeniyar Aburi ta rushe ne saboda sabani da Chukwuemeka Ojukwu kan ba gwamnonin sojoji iko.
Gowon ya ce Ojukwu ya so gwamnoni su jagoranci sojoji a yankunansu, amma gwamnati ta ki amincewa saboda ya saba wa doka.
Tsohon shugaban ya ce rashin lafiyarsa da sanarwar da Ojukwu ya fitar sun jawo rushewar yarjejeniyar Aburi tare haddasa yakin basasa.
Asali: Legit.ng
