Matatar Dangote: Buhari Zai Kaddamar Da Matatar Man Fetur Mafi Girma a Duniya

Matatar Dangote: Buhari Zai Kaddamar Da Matatar Man Fetur Mafi Girma a Duniya

  • Shugaba Muhammadu Buhari zai kaddamar da matatar danyen man fetur ta Dangote a ranar 22 ga watan Mayu na wannan shekara
  • Ana sa ran kaddamar da wannan matatar za ta kawo ci gaba ga Najeriya da kuma samar da ayyukan yi ga ‘yan kasar
  • Sannan matatar za ta samar da akalla ganga fiye da 650,000 a rana da kuma samar da tan 10m wanda zai ninka adadin danyen man da kasar ke fitarwa.

Jihar Legas- Rukunin kamfanin Dangote ya saka ranar da za a kaddamar da katafaren matatar danyen mai da ta gina a jihar Legas, wacce ta fi kowanne girma a Afrika.

Ana sa ran Shugaban Najeriya Muhammmadu Buhari ne zai kaddamar da matatar ta Dangote da za ta bada ganga fiye da 650,000 a rana a Lekki cikin jihar Legas a ranar 22 ga watan Mayu na wannan shekara.

Kara karanta wannan

Binciken masana: Yin wayan sama da mintuna 30 a mako na na mutum ya kamu da hawan jini

Dangote
Matatar Dangote, Hoto: Bloomberg
Asali: Getty Images

BusinessDay ta tattaro cewa hakan na zuwa ne bayan samun tsaiko a baya da ya hada da matsalar kudi da annobar Korona da sauran matsaloli da suka shafi kayan aiki.

Da farko an shirya kammala matatar ne a shekarar 2019 amma saboda wasu matsaloli dole aka daga zuwa wasu lokuta da dama.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kaddamar da wannan matatar zai kawo ci gaba ga ‘yan Najeriya da masu ruwa da tsaki a harkar wadanda sun dade suna jiran ganin wannan ranar.

Anyi ittifakin cewa matatar za ta rinka samar da akalla tan 10m na man fetur wanda zai kusan ninka adadin man fetur da kasar take fitarwa, zai kuma mai da kasar ta dogara da kanta da rage kashe kudade da take yi wurin tace man fetur.

Sannan ana sa ran wannan matatar za ta samar da aikin yi fiye da 4000 ga ‘yan kasar, bayan samar da bakin mai da fetur na jiragen sama da sauran sinadarai.

Kara karanta wannan

An yi nasara: WHO ta ce yanzu kam an kawo karshen annobar Korona da ta daidaita duniya

Bankin Duniya ta yi tsokaci

Bankin Duniya ya tabbatar da cewa samun wannan matatar zai rage yawan siyo man fetur da kasar ke yi a kasashen waje, Channels Tv ta ruwaito.

Mafi yawan danyen man fetur din da wannan matatar za ta samar da shi ne daga Najeriya ganin yadda Kamfanin Man Fetur ta Kasa wato NNPC ke da 20% a wannan kamfani a madadin kasar.

Kamfanin Dangote Da Sauran Kamfanonin Da Suka Tafka Asara a Farkon 2023

A wani labarin, wadannan su ne jerin kamfanonin Najeriya a ɓangarori daban-daban, wadanda suka fuskanci ƙalubale da dama a farkon shekarar 2023, saboda ƙarancin kudade da aka samu sakamakon ƙarancin kuɗi a kasar.

A rahoton da aka miƙa a kasuwar hada-hada ta Najeriya, kamfanoni shida sun samu ragowar samun kuɗin shiga wanda ya kai N46.52bn, a wata uku na farkon shekarar 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel