Jamus, Kasashen Turai sun ba Najeriya gudumuwar Naira Biliyan 20 domin gyara wuta

Jamus, Kasashen Turai sun ba Najeriya gudumuwar Naira Biliyan 20 domin gyara wuta

  • Kungiyar EU ta ba Gwamnatin Najeriya karfin tallafi domin aiwatar da rashin NESP
  • Deutsche Gesellschaft für Internationale Zusammenarbeit ta bada gudumuwar €20m

AbujaLeadership tace kungiyar EU ta kasashen nahiyar Turai ta amince ta kara bada fam miliyan €15 ga Najeriya domin tallafa wa shirin wutan NESP.

Hakan na zuwa ne a lokacin da aka bada sanarwar kulla yarjejeniyar EU da kungiyar Deutsche Gesellschaft für Internationale Zusammenarbeit, watau GIZ.

Kungiyar kasar Jamus za ta bada fam miliyan €48 domin bunkasa shirin NESP a shekara mai zuwa.

Matakin da Deutsche Gesellschaft für Internationale Zusammenarbeit ya dauka ya sa kungiyar EU ta kara gudumuwarta a kan miliyan €20 da ta bada a baya.

Rahoton yace gudumuwar da Najeriya ta samu daga hannun gwamnati da kungiyar ta Jamus da kasashen Turai da ke karkashin EU ya haura fam miliyan €48.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi Da Shugaban CAN Sun Buƙaci a Kama Musulmin Da Suka Kashe Fasto a Kano

Jamus, Kasashen Turai sun ba Najeriya gudumuwa
Na'urorin samar da wuta Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Da Legit.ng Hausa tayi lissafi a kudin Najeriya, abin da za a batar a shirin ya zarce Naira biliyan 20. Sannan gudumuwar kungiyar EU ta kai Naira biliyan bakwai.

Da take jawabi a garin Abuja a dazu, shugabar tawagar EU a kasashen ECOWAS, Cecile Tassin-Pelzer, ta tabbatar da shirin ba gwamnati wannan gudumuwa.

Misis Cecile Tassin-Pelzer tace wannan yarjejeniya ta nuna karfin alakar Najeriya da kungiyar EU.

Kungiyar ta EU da gwamnatin kasar Jamus ne suka dauki nauyin wannan shiri na NESP da zai taimaka wajen kawo karshen matsalar wuta da ake fama da shi.

Gwamnatin Najeriya za ta aiwatar da wannan aiki ne ta karkashin ma’aikatar wutar lantarki na tarayya. An kara wa’adin aikin daga Nuwamban 2022 zuwa 2023.

A ranar Alhamis, 7 ga watan Oktoba, 2021, aka ji dalilin makarantar koyon jirgin sama na rusa gidaje sama da 150 a unguwar Graceland da ke Zaria a jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Wasanni: Kasar Saudiyya ta saye kungiyar kwallon kafa ta Newcastle

Makarantar koyon jirgin saman tace rusa gidajen zai taimaki al’ummar garin Zaria. Makarantar ta bayyana haka a wani jawabi ta bakin Mista Balarabe Mohammed.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel