Zaben fidda dan takarar PDP: An gano fostocin Hayatu-Deen baje a wajen taron duk da janyewa daga tseren

Zaben fidda dan takarar PDP: An gano fostocin Hayatu-Deen baje a wajen taron duk da janyewa daga tseren

  • A safiyar yau Asabar ne aka wayi gari da labarin janyewar Mohammed Hayatu-Deen, daga tseren neman tikitin shugaban kasa na PDP
  • Sai dai duk da haka, an gano fostocin yakin neman zabensa baje a dakin babban taro na jam'iyyar adawar wanda ke gudana a Abuja
  • Wani jami'i ya ce ba aikinsu bane cirewa dan kasuwar fostocinsa, cewa kamata yayi ace shine zai sa tawagarsa su sauke hotunan daga wajen

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - An gano fostocin mai takarar shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Mohammed Hayatu-Deen, baje a wurare masu muhimmanci a filin babban taron jam’iyyar duk da cewar ya sanar da janyewarsa daga tseren.

Daily Trust ta rahoto cewa an baje kolin hotunan shahararren dan kasuwar a manyan wurare a filin wasa na Moshood Abiola, wajen zaben fidda gwanin jam’iyyar adawar tare da sauran manyan yan takara.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Babban dan takarar shugaban kasa na PDP daga arewa ya janye daga tseren

Hakazalika a gano fostocin tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, na tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, na gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, Bala Mohammed na jihar Bauchi da tsohon shugaban majalisar dattawa, Anyim Pius Anyim.

Zaben fidda dan takarar PDP: An gano fostocin Hayatu-Deen baje a wajen taron duk da janyewa daga tseren
Zaben fidda dan takarar PDP: An gano fostocin Hayatu-Deen baje a wajen taron duk da janyewa daga tseren Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Akwai wasu manyan hotunan Hayau-Deen baje a kusa da mashigin filin wasan ta bangaren yamma.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sannan akwai wasu manyan fostocin nasa guda kuma a mashigin ainahin dakin da taron ke gudana.

Yayin da tawagar sauran yan takara ke wajen, Daily Trust ta ce bata gano tawagar Hayatu-Deen ba.

Wasu magoya bayan jam’iyyar, wadanda suka zanta da manema labarai a wajen, sun ce an baje hotunan ne kafin ya janye daga tseren.

Wani jami’in jam’iyyar wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce da kamata yayi ace tsohon shugaban bankin ya bukaci magoya bayansa da su cire hotunan.

Kara karanta wannan

Yadda wasu Gwamnonin jihohi su ka yi kutun-kutun har sai da Peter Obi ya hakura da PDP

Ya ce:

“Ba aikinmu bane cire masa fostocin, tawagarsa ne ya kamata su aikata hakan.”

Da dumi-dumi: Babban dan takarar shugaban kasa na PDP daga arewa ya janye daga tseren

A wani labarin, Mohammed Hayatu-Deen, daya daga cikin manyan yan takarar da ke neman tikitin shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya janye daga tseren.

Tsohon Manajan-Darakta na rusasshen bankin FSB, ya sanar da janyewarsa daga tseren ne a cikin wata wasika da ya aikewa shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Dr Iyorchia Ayu, Daily Trust ta rahoto.

Shahararren dan kasuwar ya janye daga tseren ne yan kwanaki bayan tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, ya janye daga takarar sannan ya fice daga jam’iyyar ta PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel