'Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Fada, Sun Yi Garkuwa da Mai Martaba Sarki a Najeriya
- 'Yan bindiga sun yi garkuwa da Sarkin Olayinka da ke ƙaramar hukumar Ifelodun a Jihar Kwara, Oba Salman Aweda
- Mazauna yankin sun bayyana cewa maharan sun kai hari fadar sarkin da tsakar dare, suka tafi da shi, matarsa da wani mutum daya
- Shugaban karamar hukumar Ifelodun, Hadji Abdulrasheed Yusufya ce jami'an tsaro sun baza komarsu a dazukan yankin domin ceto su
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kwara, Nigeria - Mahara da ake zargin ‘yan bindiga ne sun sace wani mai martaba Sarki, matarsa da wani mutum guda a wani hari da suka kai da tsakar dare a ƙauyen Olayinka da ke ƙaramar hukumar Ifelodun a Jihar Kwara.
An ce sarkin, Oba Salman Aweda, na cikin sarakunan da gwamnatin jihar Kwara ta ɗaga darajarsu a baya-bayan nan.

Source: Original
Yan bindiga sun bude wuta a fadar Sarki
Rahoton Daily Trust ya ce maharan, waɗanda ke ɗauke da makamai, sun kai farmaki fadar sarkin da misalin ƙarfe 1:40 na dare ranar Asabar.
An ruwaito cewa daga zuwansu, 'yan bindigar suka riƙa harbe-harbe domin tsoratar da mazauna yankin kafin su yi awon gaba da sarkin da wasu mutum biyu zuwa inda ba a sani ba.
Wani mazaunin yankin ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa an kai harin ne da sassafe.
“Lamarin ya faru kusan ƙarfe 1:00 na dare a Olayinka. Sun kuma tafi da matarsa da wani mutum guda. Sarkin na cikin waɗanda aka ƙara musu matsayi kwanan nan,” in ji majiyar.
Wani mazaunin yakin na daban, ya bayyana harin a matsayin mai ban tsoro da sauri, kamar yadda jaridar Punch ta kawo.
“‘Yan bindigar sun zo dauke da makamai da misalin ƙarfe 1:40 na dare suka tafi da sarkin. Tsoro ya mamaye kowa, babu wanda ya iya tunkararsu,” in ji shi.

Kara karanta wannan
Shari'a ta dawo sabuwa: Saraki da tsohon gwamnan Kwara za su gurfana a kotu kan fashin Offa
An bukaci gwamnati ta dauki mataki
Da yake tabbatar da lamarin a Ora, Olora na Ora, Oba Rilwan Yekini, ya ce harin na nuna yadda matsalar tsaro ke ƙara ta’azzara a yankunan.
Ya buƙaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta shiga lamarin, yana mai cewa tsarin tsaron al’umma na buƙatar aiki tukuri da kuma samar da kayan aiki.
Matakin da jami'an tsaro suka dauka
A nasa ɓangaren, shugaban ƙaramar hukumar Ifelodun, Hadji Abdulrasheed Yusuf, ya bayyana lamarin a matsayin abin damuwa, yana mai cewa ana ci gaba da ƙoƙarin ceto waɗanda aka sace.

Source: Twitter
Yayin da ya kai ziyara yankin, ciyaman din ya ce:
“Mun damu matuƙa kuma muna ɗaukar matakan gaggawa tare da haɗin gwiwar jami’an tsaro."
Ya bayyana cewa an ƙaddamar da binciken haɗin gwiwa da aikin ceto tsakanin jami’an tsaro, masu gadin daji da ‘yan sa-kai a cikin dazuka da yankunan da ke kusa.
Yan bindiga sun sace ciyaman a Delta
A wani labarin, kun ji cewa wasu miyagun 'yan bindiga sun yi garkuwa da shugaban karamar hukumar Sapele, Hon. Bright Abeke da ke jihar Delta.
Rahotanni sun nuna cewa an girke jami'an tsaro a duk wata hanyar shiga da ta fita Sepele da nufin ceto ciyaman din cikin koshin lafiya.
A ruwaito cewa 'yan bindigar sun yi nasarar tafiya da shugaban karamar hukumar ne bayan sun yi musayar wuta da jami'an tsaronsa.
Asali: Legit.ng

