Sarkin da 'Yan Bindiga Suka Sace a Kogi Ya Rasu a cikin Daji
- An samu karin bayani game da wani basarake daga yankin Oke-Ere a jihar Kogi bayan sace shi yana aiki a gonarsa da ke yankin Yagba ta Yamma
- An rawaito cewa basaraken ya rasu a hannun masu garkuwa da mutane makonni bayan sace shi, lamarin da ya jefa al’ummar yankin cikin alhini
- An kuma rawaito cewa an sace ’yarsa da jikansa a kan hanyar Oke-Ere zuwa Egbe, yayin da daga baya aka ceto yaron cikin ƙoshin lafiya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kogi - Wani basarake a Oke-Ere da ke ƙaramar hukumar Yagba ta Yamma a jihar Kogi, Adebayo Samuel ya rasu a hannun masu garkuwa da mutane.
An sace Samuel ne ranar 21 ga Afirilun 2026 da misalin ƙarfe 10:00 na safe yayin da yake gudanar da ayyukan noma a wata gona da aka noma a yankin Odo-Ere.

Source: Twitter
Wata majiya ta tabbatar wa Legit labarin ne makonni bayan wasu da ake zargin ’yan bindiga ne suka sace shi yayin da yake aiki a gonarsa.
Sarkin da aka sace ya rasu
Majiyoyi daga iyalansa da al’ummar yankin sun shaida wa Legit cewa basaraken ya je shuka amfanin gona a gonar da wani ma’aikacin yankin ya taimaka masa wajen gyarawa kafin ’yan bindigar su mamaye yankin su yi awon gaba da shi.
A cewar majiyoyin, ma’aikacin gonar ya samu damar tserewa daga baya ya dawo cikin gari domin sanar da mazauna yankin cewa wasu da ake zargin ’yan bindiga ne suka sace basaraken.
“Ya je gona da safe kamar yadda ya saba yi a kullum,”
Wani mazaunin yankin ya shaida wa Legit
“Mutumin da ya raka shi gonar ne ya dawo ya sanar da al’umma cewa masu ɗauke da makamai sun sace Baba daga gonar.”
Mazauna yankin sun ce sace Sarkin ta jefa al’umma cikin fargaba, inda iyalai da shugabannin yankin suka shiga neman hanyoyin ganin an kuɓutar da shi.
Sai dai wannan fata ya kare a safiyar Juma’a, 8 ga Mayun 2026 bayan rahotanni sun bayyana cewa Samuel ya rasu a hannun masu garkuwa da mutanen.

Source: Original
Ana jimamin rasuwar sarkin
Biyo bayan samun labarin rasuwar sarkin, al'umma da dama sun shiga damuwa tare da yi masa addu'o'i, wata majiya ta shiada cewa:
“Dukkan garin na cikin alhini,”
“Mutane sun addu’ar ya dawo lafiya, amma yanzu iyalansa sun shiga baƙin ciki bayan samun labarin cewa ya mutu a hannun masu garkuwa da shi.”
Har zuwa lokacin hada wannan rahoton, dukkan ƙoƙarin da Legit ta yi domin samun martani daga kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Saliu Oyiza Afusat ya ci tura.
An kama mai taimakon 'yan bindiga
A wani labarin, mun kawo muku cewa rundunar 'yan sandan jihar Katsina sun tabbatar da kama wani matashi da ake zargi da taimakon 'yan bindiga.
Bayan dogon bincike da tambayoyi da aka masa, an samu matashin da wasu kayayyaki da suka hada da abubuwan da aka ce na tsafi ne.
Rahotanni sun nuna cewa da zarar an kammala bincike game da shi rundunar 'yan sanda za ta gurfanar da shi a gaban alkali domin a hukunta shi.
Asali: Legit.ng

