Guguwa ta kashe mutum 2, ta lalata gidaje 380 a Sokoto

Guguwa ta kashe mutum 2, ta lalata gidaje 380 a Sokoto

- Guguwar iska a daren ranar Lahadi, 16 ga watan Yuni ta hallaka wani tsoho dan shekara 95 da wani matashi a wasu kauyuka da ke karamar hukumar Shagari na jihar Sokoto

- Guguwar ta kuma lalata gidaje 380

- Yankunan da abun ya shafa sun hada da Shagari, Kaura, Wanke, Gadara, Sage, Kajiji da kuma Kesoje

Wata guguwar iska a daren ranar Lahadi, 16 ga watan Yuni ta hallaka wani tsoho dan shekara 95 da wani matashi a wasu kauyuka da ke karamar hukumar Shagari na jihar Sokoto.

Guguwar ta kuma lalata gidaje 380. An tattaro cewa mutanen sun mutu ne a daya daga cikin ginin da iskar ta lalata.

Daraktan hukumar bayar da agajin gaggawa na jihar, Mustapha Umar, a jiya Litinin, 17 ga waatan Yuni yace yankunan da abun ya shafa sun hada da Shagari, Kaura, Wanke, Gadara, Sage, Kajiji da kuma Kesoje.

Ya bayyana cewa jimlan gidaje 380 ne abun ya shafa inda wasu daga cikinsu suka ruguje baki daya.

Yayinda yake jaje ga wadanda abun ya shafa, yace gwamnatin jihar za ta fara rabon kayayyakin agaji a gare su nan ba da jimawa ba.

KU KARANTA KUMA: Magani a gonar yaro: Magunguna 18 da Zogale ke yi a jikin Dan Adam

A wani lamari makamanci haka, Legit.ng ta rahoto cewa Alhaji Nasiru Lawal, dan majalisar dokokin jihar Zamfara, ya bayyana cewar wata iskar guguwa mai karfi ta yi barna a gidaje fiye da 1000 a karamar hukumar Bungudu da ya ke wakilta.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa lamarin ya faru ne da yammacin ranar Lahadi.

Da ya jagoranci 'yan jarida domin gane wa idanuwansu barnar da guguwar da ta yi, Bungudu ya bayyana lamarin da cewa abin takaici ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng