An Samu Galaba kan Ta’addanci, Hatsabibin Dan Bindiga Ya Shiga Hannu a Kaduna
- Dakarun Operation Fansan Yamma sun kama wani da ake zargin dan bindiga ne a Birnin Gwari tare da kwato manyan makamai
- Majiyoyi sun tabbatar da cewa daga cikin abubuwan da aka samu a wurinsa akwai bindigar AK-47, wayoyi da tabar wiwi
- Binciken farko da jami’an tsaro suka yi ya gano hotunan da ake zargin mutumin yana sanye da kayan soji tare da daukar hoto da bindigar PKT
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Birnin Gwari, Kaduna - Dakarun rundunar Operation Fansan Yamma sun kama wani mutum da ake zargin dan bindiga ne a jihar Kaduna.
An cafke Ibrahim Adamy ne yayin wani samame na binciken ababen hawa a karamar hukumar Birnin Gwari da ke Kaduna a yankin Arewa maso Yamma.

Source: Twitter
Majiyoyin tsaro sun bayyana wa Zagazola Makama cewa an kama wanda ake zargin ne da misalin karfe 6:04 na yammacin ranar 8 ga Mayun 2026.
Bayanai kan dan bindigan da aka kama
Rahoton ya ce jami’an Bataliya ta 2 da ke aiki a sansanin FOB Dogon Dawa ne suka kafa shingen bincike a yankin Damari lokacin da suka tare wani mutum da ke kan babur.
An gano sunan wanda ake zargin da Ibrahim Adamu mai shekaru 32 a duniya da muggan makamai da wasu abubuwa masu hatsari.
Majiyoyin sun ce yayin binciken da aka yi masa, an kwato mujallar bindigar AK-47 guda daya, wayoyin hannu uku, tabar wiwi da wasu kayayyaki daga hannunsa.
Wasu abubuwan da aka gano a wurinsa
Binciken farko da jami’an tsaro suka gudanar a cikin wayoyinsa ya gano wasu hotuna masu tayar da hankali.
Rahotanni sun nuna hotunan na nuna wanda ake zargin sanye da kayan kama da na soja yana daukar hoto tare da bindigar PKT da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne.
Jami’an sojojin sun ce an kai wanda ake zargin tare da kayayyakin da aka kwato zuwa hedkwatar bataliya domin ci gaba da bincike da daukar matakan da suka dace.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun nuna rashin imani, sun bude wa mutane wuta a wurin jana'iza a Filato

Source: Original
Halin da ake ciki a yankin Birnin Gwari
Rundunar sojin ta kara da cewa duk da yankin na cikin kwanciyar hankali, har yanzu akwai bukatar ci gaba da sanya ido saboda yanayin tsaro mai cike da rashin tabbas.
Operation Fansan Yamma na ci gaba da gudanar da hare-hare da ayyukan tattara bayanan sirri a sassan Arewa maso Yamma domin dakile ayyukan ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane da sauran miyagun laifuka, cewar Punch.
Sojoji sun kama makamai a Kaduna
A wani labarin, mun ba ku rahoton cewa dakarun sojojin Najeriya sun yi nasarar kama wata mota a makare da makamai masu hadarin gaske a hanyar Manchok–Jos.
An kama mutane bakwai da ake zargi da hannu a safarar makaman da ake hasashen ana shirin ta'addanci da su a yankunan jihohin Kaduna da Plateau.
Jami'an tsaron sun yi nasarar kwato harsasai 569 da sauran kayan fashewa da aka duƙunƙune a cikin motar ɗauke da fasinjoji.
Asali: Legit.ng
