Malami zai San Matsayar Dukiyoyinsa da Gwamnati Ta Kwace a Kotu

Malami zai San Matsayar Dukiyoyinsa da Gwamnati Ta Kwace a Kotu

  • Kotun ɗaukaka ƙara ta jinkirta yanke hukunci kan buƙatar tsohon Ministan shari'a, Abubakar Malami, ta neman izinin ɗaukaka ƙara kan ƙwace kadarorinsa
  • Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa a kasar nan, EFCC na zargin Malami ya samo wasu kadarori 57 da ake takaddama a kansu ta haramtattun hanyoyi
  • Lauyoyin ɓangarorin biyu sun yi musayar yawu kan jinkirin shigar da ƙarar da kuma dokar sauraron shari’un rashawa cikin gaggawa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta ajiye hukunci kan wata buƙata da tsohon Antoni Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami.

Abubakar Malami ya shigar da kara domin neman izinin ɗaukaka ƙara kan hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke game da ƙwace wasu kadarori da ake alaƙanta shi da su.

Kara karanta wannan

Alkawarin da sabon ministan makamashi ya dauka kan faduwar turakun wutar lantarki

Abubakar Malami zai san makomarsa kan kwace kadarorinsa
Abubakar Malami, tsohon Antoni Janar a Najeriya Hoto: Abubakar Malami SAN
Source: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa kwamitin alkalai uku na kotun, ƙarƙashin jagorancin Mai shari’a Abba Mohammed, bai bayyana ranar yanke hukuncin ba, sai dai ya ce za a sanar da ɓangarorin da zarar hukuncin ya kammala.

Abubakar Malami zai kalubalanci kwace kadarorinsa

Malami, ta hannun lauyansa Joseph Daudu (SAN), na ƙalubalantar hukuncin da Mai shari’a Joyce Abdulmalik ta yanke a wata shari’a da ta shafi ƙwace kadarori 57 da ake zargin suna da alaƙa da haramtattun ayyuka.

Tun da farko dai, hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta samu umarnin wucin gadi na ƙwace kadarorin a farkon shekarar nan a shari'ar da ta ke yi da tsohon Ministan.

EFCC ta nemi kotu ta watsar da bukatar Malami
Abubakar Malami, tsohon Ministan shari'a a Najeriya, hedkwatar EFCC a Abuja Hoto: Abubakar Malami SAN/Economic and Financial Crimes Commission
Source: Twitter

Da yake gabatar da ƙorafin a gaban kotun ranar Alhamis 7 ga watan Mayu, 2026, Daudu ya bayyana cewa buƙatar da suka shigar ta haɗa da neman ƙarin lokaci domin neman izinin ɗaukaka ƙara, neman izinin ɗaukaka ƙarar da kuma ƙarin lokacin shigar da ƙarar.

Kara karanta wannan

Tofa: Kotu ta bada umarnin kwace wasu kadarorin tsohon ministan Najeriya, Sylva

Lauyan ya ce jinkirin da aka samu wajen shigar da ƙarar ya samo asali ne daga lokacin da aka ɗauka ana jiran kwafin sahihin hukuncin kotun ƙasa.

EFCC ta nemi a watsar da bukatar Malami

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa lauyan EFCC, Jibrin Okutepa, ya buƙaci kotun ta yi watsi da buƙatar Malami, yana mai cewa babu wata gamsasshiyar hujja da ta hana shi shigar da ƙarar a kan lokaci.

Okutepa ya bayyana cewa shari’ar na ƙarƙashin dokar sauraron shari’un rashawa da laifuffkan kuɗi, don haka bai dace a tsaya ana sauraron ƙorafe-ƙorafen da ba su shafi ainihin shari’ar ba.

Ya shaida wa kotun cewa ana zargin an samo kadarorin ne ta hanyar damfara lokacin da Malami yake riƙe da muƙamin Antoni Janar na Tarayya.

Tsohon ministan shari'a ya magantu kan kadarorinsa

A baya, mun wallafa cewa tsohon babban lauyan gwamnatin tarayya kuma Ministan shari'a, Abubakar Malami, na fuskantar shari'a a gaban kotu kan zargin wawashe dukiyar jama'a.

Abubakar Malami ya gabatar da bukata a gaban kotu kan yunkurin da hukumar EFCC ke yi na kwace wasu kadarorinsa da ta ce an samu ta haramtacciyar hanya, inda ya ce dukiyar halal ce.

Tsohon Ministan ya sanar da kotu yadda ya samu kudadensa a tsawon shekarun da ya kwashe yana aiki da harkokin kasuwanci tare da neman a shiga tsakanin EFCC da karbe masa kadarori.s

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng