Dan Majalisar Amurka Ya Harzuka kan Harin Plateau, Ya Gayawa Trump Matakin Dauka kan Najeriya

Dan Majalisar Amurka Ya Harzuka kan Harin Plateau, Ya Gayawa Trump Matakin Dauka kan Najeriya

  • 'Dan majalisa a kasar Amurka, Riley Moore, ya yi martani mai zafi kan kisan da wasu 'yan bindiga suka yi a jihar Plateau
  • Riley Moore ya soki gwamnatin Najeriya wajen gaza kare 'yan kasarta amma tana zuwa aikin dakile juyin mulki a wata kasar daban
  • Dan majalisar ya bukaci gwamnatin Shugaba Donald Trump da ta dauki mataki kan Najeriya saboda zubar da jinin ake yi

​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Washington, Amurka - Wani ɗan majalisa a Amurka, Riley Moore, ya yi kira ga gwamnatin Shugaba Donald Trump kan kashe-kashe a Najeriya.

Riley Moore ya bukaci gwamnatin Trump da ta ɗauki abin da ya kira "mataki mai ƙarfi" don kare mabiya addinin Kirasta a Najeriya sakamakon sababbin hare-hare a jihar Plateau.

Riley Moore ya soki kisan Kiristoci a Najeriya
Dan majalisar Amurka, Riley Moore na jawabi a wajen taro Hoto: @RepRileyMoore
Source: Twitter

Riley Moore ya yi wannan kiran ne a cikin wata sanarwa da ya sanya a shafinsa na X ranar Alhamis, 7 ga watan Mayun 2026.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun nuna rashin imani, sun bude wa mutane wuta a wurin jana'iza a Filato

'Yan bindiga sun kashe mutane a Plateau

Moore ya yi kiran ne yayin da yake martani ga rahotanni daga ƙaramar hukumar Barkin Ladi da ke jihar Plateau, inda wasu mahara suka kai wa masu zaman makoki hari yayin wani taron jana’iza a ranar Laraba.

Ana fargabar cewa an kashe mutane da dama yayin da wasu da dama suka ji rauni bayan da rahotanni suka ce maharan sun buɗe wa mazauna yankin wuta, waɗanda suka taru don binne mutane bakwai da aka kashe a baya a yankin.

Sai dai, rundunar yan sanda ba ta riga ta tabbatar da harin a hukumance ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

Riley Moore ya soki gwamnatin Najeriya

A cikin sanarwar tasa, Moore ya kwatanta kai daukin ayyukan soja da Najeriya ta yi a maƙwabciyarta Jamhuriyar Benin lokacin da aka yi ƙoƙarin juyin mulki da abin da ya siffanta da gazawar gwamnati wajen dakatar da kashe-kashe a sassan jihar Plateau.

Kara karanta wannan

"Zai fi na baya"; Donald Trump ya sake yin babbar barazana ga Iran

"Lokacin da na ziyarci Najeriya, gwamnati ta mayar da martani cikin gaggawa don dakile juyin mulki a Benin."
"Shirye-shiryen Najeriya na shiga tsakani don dakatar da mummunan hari a wata ƙasa, yayin da take zuba ido ana wulaƙanta nata yan ƙasar mabiya Kirasta, ya sa waɗannan munanan al’amura da ke faruwa a jihar Plateau su zama abin takaici da ba za a amince da su ba."

- Riley Moore

Moore ya yi zargin cewa ana kashe Kiristoci

'Dan syasar ya yi zargin cewa Kiristoci da suka taru don jana’iza "wasu tsagerun yan ta’adda sun kashe su cikin rashin imani," yana mai ƙarawa da cewa gwamnatin Najeriya ta kasa ɗaukar mataki duk da gargaɗin da aka bayar tun da wuri na yiwuwar kai hare-haren.

"Gwamnatin Najeriya tana da ikon kakkabe ta’addanci da dakatar da kisan yan ƙasarta. Amma, duk da samun gargaɗi tun da wuri na hare-haren da ke tafe, ba a ganinsu yayin da ake kashe Kiristoci saboda addininsu, kamar tumakin da aka kai wurin yanka. Ya isa haka."

Kara karanta wannan

Dan majalisa a Borno ya fashe da kuka, ya roki a bari ya sake komawa kujerarsa

- Riley Moore

Riley Moore ya soki gwamnatin Najeriya
Dan majalisar Amurka, Riley Moore Hoto: @RileyMoore
Source: Twitter

Wace shawara ya ba Shugaba Trump?

Riley Moore ya ci gaba da cewa ya ji daɗi da gwamnatin Trump ta bayyana kariyar Kiristoci a Najeriya a matsayin wani ɓangare na dabarunta na yaƙi da ta’addanci, yana mai ƙara da cewa:

"Yanzu haka, ina buƙatar gwamnatin Trump da ta ɗauki mataki mai ƙarfi don kare ’yan’uwanmu maza da mata Kiristoci da ba su ji ba, ba su gani ba a yankin tsakiyar Najeriya na Najeriya, inda nan ne matattarar kisan kiyashi da ake yi wa Kiristoci."

Trump ya yi wa Iran barazana

A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi barazana ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Trump ya gargadi Iran cewa ko dai ta yarda da yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin ko kuma ta fuskanci sababbin hare-haren bama-bamai na Amurka masu tsanani.

Gargadin na Trump na zuwa ne yayin da ake sa ran kulla yarjejeniyar da za ta kawo karshen yakin da ake yi a Gabas ta Tsakiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng