Dan Tsohon Gwamna, Bello Ya Fadi Matsayarsa kan Rigimar El Rufai da Uba Sani da Ake Yi

Dan Tsohon Gwamna, Bello Ya Fadi Matsayarsa kan Rigimar El Rufai da Uba Sani da Ake Yi

  • Hon. Bello El-Rufa'i ya ce ba ya jin daɗin rikicin da ke faruwa tsakanin mahaifinsa, Nasir El-Rufa'i, da gwamna Uba Sani, yana fatan zaman lafiya
  • Bello ya bayyana cewa ba ya tsammanin suna rigima da juna, domin ba wanda ya fito ya zagi dayan a gaban shi ko ya bayyana wata gaba
  • Dan majalisar ya ce bincike ba laifi ba ne, amma idan ana yin sa domin tozarta wani ko zalunci, Allah ne kawai zai hukunta mai aikata hakan

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Kaduna - Yayin da ci gaba da samun sabani tsakanin Nasir El-Rufa'i da Uba Sani, Hon. Bello El-Rufai ya yi tsokaci.

Hon. Bello El-Rufa’i wanda ɗa ne ga tsohon gwamnan Kaduna kuma ɗan majalisa, ya bayyana ra’ayinsa kan wannan rikicin.

Kara karanta wannan

Dan El Rufai ya fadi matsayarsa kan bincikar mahaifinsa ya ba da shawara

Dan El-Rufai ya yi tsokaci kan rigimar mahaifinsa da Uba Sani
Hon. Bello El-Rufai ya magantu kan rigimar Nasir El-Rufai da Uba Sani. Hoto: @B_ELRUFAI.
Asali: Twitter

Bello ya magantu kan rigimar El-Rufai, Uba Sani

A wata hira da aka yi da shi a shirin Mahangar Zamani na BBC Hausa, Bello ya ce ba ya jin daɗin abin da ke faruwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hon. Bello El-Rufai ya ce dukkansu biyu manyan mutane ne a rayuwarsa wanda ba zai manta da su ba kuma suna da tasiri.

"Ba daɗi mana, a cikinsu ba wanda ya ce mani komai kan lamarin, kawai na gane cewa yanzu ba da ba ne.
"Jama'a suna so abin ya zama kamar Dramendra da Amitabh Bachchan na fim ɗin Indiya, har kira na wasu ke yi kan lamarin."

- Bello El-Rufai

'Ban san musabbabin rikicin ba' - Bello El-Rufai

Bello ya ce rikici tsakanin mutane ba sabon abu ba ne, domin "aure na rabuwa, abokai su daina abokantaka," amma ya kamata zumunci ya kasance koda bayan sabani.

Ya kuma ce bai san musabbabin rikicin ba, domin bai taɓa jin ɗaya daga cikinsu yana zagin ɗayan ba.

Kara karanta wannan

'Na so zama soja': Gwamnan PDP ya fadi burinsa yayin jimamin mutuwar yayansa

A cewarsa, ba ya ma san ko fadan da ake zargin suna yi gaskiya ne kamar yadda ake yayatawa.

Ya kuma ce wasu mutane ne ke ƙara rura wutar rikicin fiye da yadda yake a zahiri saboda kawai su yada labarai kan haka.

Ko Bello zai iya sasanta El-Rufai, Uba Sani?

"Wallahi ba aikina ba ne, aikina shi ne mayar da hankali kan taimaka wa mutanen mazabar Kaduna ta Arewa."
"A wurina, ba wanda ya kai Mallam Nasiru a siyasance, aikin shi kawai yake sawa a gaba, Kuma uba uba ne."

- Bello El-Rufai

Ya kuma ce yana girmama gwamna Uba Sani, don haka ba zai ce komai maras kyau a kansa ba duba yadda yadda suke da shi tun a baya.

An bukaci Ribadu ya taka wa El-Rufai birki

Kun ji cewa Kungiyar kare dimukradiyya, TAN ta bukaci Nuhu Ribadu da ya dakatar da Nasir El-Rufai kan wasu kalamansa.

Kara karanta wannan

Hadimin Tinubu ya yi wa El Rufai wankin babban bargo, ya fadi wani sirrinsa

El-Rufai ya soki gwamnatin Bola Tinubu yana kwatanta ta da mulkin soja, tare da zargin Gwamna Uba Sani da karɓar kudi daga Gwamnatin Tarayya a asirce.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.