Bukatar Hukumar DSS ga Babbar Kotu kan ci Gaba da Shari’ar El Rufai a Abuja

Bukatar Hukumar DSS ga Babbar Kotu kan ci Gaba da Shari’ar El Rufai a Abuja

  • Hukumar DSS ta tura bukata ta musamman ga kotu kan ci gaba da shari'ar da ake yi game da zargin Malam Nasir El-Rufai
  • DSS ta nemi kotu ta ɓoye sunayen shaidu a shari’ar Nasir El-Rufai, tana mai cewa hakan na da muhimmanci domin kare lafiyarsu
  • El-Rufai ya musanta tuhume-tuhume guda biyar da ake yi masa kan zargin sauraron tattaunawar waya ba tare da izini ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Hukumar tsaro ta farin kaya, DSS ta tura bukata ta musamman ga babbar kotun tarayya kan shari'ar tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai.

An gurfanar da tsohon gwamnan Kaduna a gaban kotu kan tuhume-tuhume guda biyar da suka shafi zargin samun damar leken asirin tattaunawar waya ba tare da izini ba.

DSS ta roki kotu kan shari'ar El-Rufai
Mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu da Malam Nasir El-Rufai. Hoto: Nuhu Ribadu, Nasir El-Rufai.
Source: Twitter

Bukatar hukumar DSS ga kotu a Abuja

Kara karanta wannan

Kotu ta soke belin tsohon hadimin El Rufai, an kara ingiza keyarsa zuwa kurkuku

Hukumar DSS ta bukaci kotun da ke Abuja ta ba ta damar ɓoye sunayen wasu shaidu biyu da ake sa ran za su bayar da shaida a shari’ar Nasir El-Rufai, cewar TheCable.

Bayan karanta masa tuhume-tuhumen, El-Rufai ya musanta dukkan laifukan da ake tuhumarsa da su inda ya ke zargin akwai kullalliyar kan zarge-zargen da ake yi masa.

Lauyan DSS ya roki kotu ta ba da damar shaidun su bayar da shaida a ɓoye saboda dalilan tsaro da kare lafiyarsu duba da yadda shari'ar ke da girma a yanzu.

DSS ta gurfanar da El-Rufai a kotu kan zargin leken asiri
Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai. Hoto: Nasir El-Rufai.
Source: Twitter

Lauyan El-Rufai ya yi fatali da bukatar DSS

Sai dai lauyan El-Rufai ya yi adawa da wannan bukata inda ya ke ganin an saba dokar kasar Najeriya wanda hakan ka iya jawo matsala a shari'ar da ake yi.

Lauyan ya bayyana cewa kundin tsarin mulki ya ba wanda ake tuhuma damar sanin shaidun da ke tuhumarsa wanda zai iya ba shi damar samun wasu hujjoji.

Ya kuma ce DSS ba ta gabatar da wata hujja da ke nuna cewa El-Rufai na iya barazana ga shaidun ba.

Bangaren tsaro ya kuma ƙi amincewa da bukatar a gabatar da cikakken bayanan shari’ar ga wanda ake tuhuma domin shirin kare kansa.

Kara karanta wannan

El Rufai: DSS ta gurfanar da tsohon gwamnan Kaduna kan zargin leken asiri

Haka kuma Malam Nasir El-Rufai ya shigar da bukatar beli, wanda DSS ta ce ba za ta hana shi ba.

A ƙarshe, kotu ta ɗage sauraron karar zuwa ranakun 18, 19 da 20 na watan Mayu domin ci gaba da shari’ar, cewar rahoton Punch.

El-Rufai ya zargi ana kulla masa makarkashiya

A baya, mun ba ku labarin cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai, ya nuna damuwa kan sabon shirin da ya yi zargin ana kullawa a kansa.

Tsohon gwamnan Kaduna ya nuna cewa ana yin wata kulla-kulla domin ganin an ci gaba da tsare shi a hannun hukumomi saboda wasu bukatun gwamnati mai ci.

Nasir El-Rufai ya yi zargin cewa ana kokarin alakanta da wasu laifuffuka domin ganin ya gaza samun beli lamarin da ke kara jawo maganganu da zargin akwai siyasa a ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.