Fitaccen Mawakin Gargajiya a Arewa, Mai Asharalle Ya Yi Bankwana da Duniya

Fitaccen Mawakin Gargajiya a Arewa, Mai Asharalle Ya Yi Bankwana da Duniya

  • Gwamna Dikko Radda ya nuna alhini kan rasuwar fitaccen mawakin gargajiyar Hausa wanda ya rasu bayan fama da jinya a Katsina
  • Marigayin ya bar mata uku da yara 22 tare da jikoki 46, yayin da gwamnati ta bayyana shi a matsayin ginshikin al’adun Hausawa
  • Gwamna Radda ya ce Surajo Mai-Asharalle ya taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa wakokin Asharalle da kiɗan farauta, inda aka san shi da Farautan Katsina

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Katsina - Gwamnan Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya bayyana matukar alhini kan rasuwar shahararren mawakin gargajiyar a Arewa.

Majiyoyi sun ce Alhaji Surajo Mai-Asharalle, ya rasu ranar Alhamis, 30 ga Afrilu, 2026, bayan doguwar jinya a Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Katsina.

Radda ya yi jimami kan rashin mawakin Hausa
Gwaman Dikko Umaru Radda na jihar Katsina. Hoto: Dikko Umaru Radda.
Source: Facebook

Legit Hausa ta samu wannan sanarwa ce daga shafin X na gwamnatin jihar Katsina wanda Kaulaha Mohammed ya sanya wa hannu.

Kara karanta wannan

Kwana ya kare: Shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar Benuwai, Agbgbo Ode ya rasu

Suraji Mai Asharalle: Gwamna Radda ya yi ta'aziyya

Marigayin ya rasu ya bar mata uku da yara 22 tare da jikoki 46, Gwamna Radda ya bayyana marigayin a matsayin babban gwarzon al’adu.

An ce marigayin ya sadaukar da rayuwarsa wajen karewa da bunkasa wakokin gargajiyar Hausa wanda ya kara inganta al'adar ƙasar Hausa da kuma kara zaman lafiya a yankin.

Ya ce Surajo Mai-Asharalle ya yi fice tun daga shekarun 1990 saboda salon wakokinsa na Asharalle da kuma jagoranci a bangaren kiɗan farauta, abin da ya sa aka ba shi lakabin Farautan Katsina.

Gwamna Radda ya kara da cewa marigayin almajirin fitaccen mawaki Dakta Mamman Shata ne, wanda ya taba karrama shi da sarautar Garkuwan Mawaƙa saboda gudunmawar da ya bayar ga harkar waka.

Sanarwar ta ce:

“Alhaji Surajo ya kasance mai kare al’adunmu wanda wakokinsa suka taimaka wajen adana tarihi da kuma zaburar da al’umma daban-daban."
Gwamna Radda ya tura sakon ta'aziyya ga iyalan marigayi Mai Asharalle
Gwamna Dikko Umaru Radda da marigayi Surajo Mai Asharalle. Hoto: @KatsinaStateNig.
Source: Twitter

'Rashin da Katsina da Hausawa suka yi'

Gwamna Radda ya bayyana rasuwar mawakin a matsayin babban rashi ga Katsina da daukacin al’ummar Hausawa, yana mai cewa an rasa mutum mai daraja da kuma wata alama ta asalin al’adu.

Kara karanta wannan

A gaban Mai Mala Buni: Gwamnan Katsina ya kaddamar da titi mai nisan kilomita 39

A madadin gwamnati da al’ummar Katsina, gwamnan ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan marigayin da masu harkar waka, tare da addu’ar Allah ya jikansa da rahama.

Gwamnan ya ba iyalan marigayin hakuri juye wannan babban rashi da suka yi duba da irin gudunmawa da ya bayar da a'adun Hausawa inda ya yi masa addu'ar samun rahama a gobe kiyama.

An nada ɗan Gwamna Dikko Radda sarauta

A wani labarin, an ji cewa mai martaba Sarkin Katsina, Abdulmumini Kabir Usman, ya jagoranci nadin sarautar dan Gwamna Dikko Umaru Radda a jihar.

Taron naɗin sarautun ya samu halartar gwamnoni, sarakuna da manyan baƙi daga sassan Najeriya da kuma jamhuriyar Nijar makwabciya.

Sarkin Katsina ya yi kira ga jama’a su rungumi zaman lafiya, haɗin kai da kyawawan ɗabi’u domin tabbatar da ci gaba da zaman lafiya a al’umma

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.